Kakakin kamfen din takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, Abdulmumini Jibrin ya ce sakamakon zaɓen gwajin da NOI ta gudanar a yanar gizo tarkace bola ne da ya kamata a tattara su a watsar bola fomin ba shi da wani amfani.
Jibrin ya ce ” ina son kowa ya sani cewa Kwankwaso ya gama da yankin Arewa, burbuɗin tsirarun kuri’u da za mu harhaɗa ya ci zaben shugaban kasa kawai zamu nema daga yankin kudu, amma wai wasu can sun gudanar da zaɓen gwaji har Peter Obi na LP ne zai ci, an gaya musu haka ake yin zaɓen.
Jibrin ya kara da cewa, Kwankwaso zai kada Tinubu da Atiku a zaben shugaban kasa mai zuwa domin kuwa duk da Tinubu mutumin kirkine kuma gogan siyasa, amma yana jam’iyyar da bata dace da shi ba.
” NOI sun fidda rahoto irin haka a 2015 cewa Goodluck Jonathan ne zai yi nasara a zaɓen 2015, amma ai ba haka ya zama ba.
Shi ko Daniel Bwala na ɓangaren Atiku Abubakar, PDP cewa yayi ƴan Peter Obi na cikin mafarki ne haryanzu ko kuwa yace sun zauce.
” Sun ɗauka a yanar gizo a zaɓe, duk da cewa wai wannan zaɓen gwaji da NOI suka gudanar a yanar gizo hayaniya ce kawai.
Bayo Onanuga na Tinubun APC cewa yayi ” Wannan zaɓen gwaji da aka yi wai Peter Obi ne zai ci zaɓen shugaban kasa tarkacen shirme ne da ya cancanci a tarkata shi a jefar da su a kwandon shara kawai.
Obi ne kan gaba
Cibiyar NOI da ya gudanar zaben gwaji kan ƴan takarar shugaban kasa na jam’iyyun kasar nan, ya bayyana cewa sakamakon zaɓen gwaji da cibiyar ya yi ya nuna cewa Peter Obi na jam’iyyar LP ne zai yi nasara a zaɓe.
Peter Obi na jam’iyyar LP ne ke kan gaba cikin jerin ƴan takarar da aka yi gwajin akan su.
Sakamakon zaɓen gwajin ya nuna cewa da za a gudanar da zaɓen shugaban kasa yau a Najeriya, Peter Obi ne zai yi nasara.
” Akalla kashi 21 cikin 100 na mutanen Najeriya duk Peter Obi za su zaɓa. Kashi 13 cikin 100 ne za su zaɓi Atiku Abubakar da Bola Tinubu da suka yi canjaras. Shi ko Kwankwaso kashi 3% ne kacal za su zaɓe shi.” In ji sakamakon zaɓen gwajin NOI.
Discussion about this post