Gwamnan jihar Ribas, Nyesome Wike ya bayyana cewa akwai wani a fadar shugaban kasa wanda shune ya ke ɗaure wa shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu da ɗan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar gindi.
Wike ya ce nan ba da dadewa ba zai fallasa ko wanene wannan mutumin kowa ya san shi.
” Ina so Ayu da Atiku su sani cewa wanda suke takama da shi a fadar shugaban kasa da yake daure musu gindi suke abinda suka dama a PDP ba zai iya kai su ga ci ba, domin shima ɗan takarar da ya mara wa baya a APC ya faɗi zaɓe.
” Sannan kuma nan ba da daɗewa ba zan faɗi sunnan sa kowa ya sn shi.
Wuke ya ce ” Ba shugaban kwamitin dattawa ba ne ya dame mu, shugabancin jam’iyyar ce muke so a maido shi yankin Kudu. Dama kwamitin dattawa ay shawara ce kawai take iya bayarwa, gudanar da ayyukan jam’iyyar yana ƙarƙashin shugaban jam’iyyar ne.
” Ina so in sanar muku cewa mutum biyu ne ke gudanar da shugabancin PDP, Ayu da Atiku. Yadda suke so suke yi, saboda sun da wanda ya ke daure musu gindi a fadar shugaban kasa.
Wike ya kara da cewa ” Wai shikenan yankin kudu ba su da ta cewa kenan a gudanarwar PDP? Mu ina ruwan mu da shugaban BOT, shugaban jam’iyya muka ce a cire a saka ɗan yankin kudu, suma ayi da su.
Idan ba a manta ba, Wike ya caccaki Ayu a cikin makon jiya inda ya yi zargin cewa su ne suka tsamo shi daga cikin kwata, suka wanke shi tas suka bashi jam’iyyar ya shugabanta.
A martanin da Ayu ya maida masa, ya ce Wike yaro ɗan karami da bai san yadda aka gina PDP ba ‘, yana so yanzu ta sha romon bargon da bai san yadda aka yo farautar dabbar ba.
Discussion about this post