Wannan fa ba shine karo na farko ba, duk lokacin da jarabawa ta ambaliyar ruwa ya mamaye jihar Jigawa, Gwamna Badaru ya kan tsallake ya bar jiha, sannan kuma ya ki ba da umarnin yin abin da ya dace ga kowa. Ya kan kyale mutane ne cikin halin ha’ula’i da ƙaƙanikayi.
Haka ta faru a 2018, 2020 ga kuma wadda take faruwa a yanzu, wanda tafi kowacce hatsari.
Gwamn Badaru ya saba rantsuwar da yayi na kare rayuka da dukiyoyin mutanen Jigawa.
Mutanen Jigawa, musamman sassan kasar Hadejia da sassan Birnin Kudu, Gwaram, Miga, Jahun suna cikin ibtila’in da ta wuce ta yaki.
A yanzu babu mai iya gayama maka yawan mutanen da suke cikin wannan ibtila’in.
Asarar rayukan da a keyi, koda yaki a keyi a tsagaita wuta don a ceci mata kananan yara, amma fa wannan ambaliya babu ruwan ta.
Garuruwan da ruwa ya mamaye suna da yawa kuma har yanzu ruwan barna yakeyi.
Kusan dukkannin muhimman hanyoyin Jigawa sun karye, an raba mutane da wannan ibtila’i ta shafa da ma inda zasu samu su tsira.
Duk inda kaga ana yin jinga ko fito da mutane daga garin da ruwa ya mamaye, al’ummah ne keyi da kanta ba bu hannun gwamna da gwamnati a ciki.
Har yanzu, babu maganar nuna kulawa, hatta sakon na murya da ga gwamna ta nuna alhini, bai aiko wa yan Jigawa ba a duk inda suke.
Duk shugaban da yasan darajar mutanen sa, yasan girman alkawari da rantsuwar da yayi, ya kamata ya waiwai ci mutanen sa a ko ina yake.
Babu wani jami’in da yayi w mutanen Jigawa a ina Gwamna yake, me ya hana shi yanke hutun sa da fuskantar bala’in da ke addabar mutanen jahar sa.
Wasu gwamnonin jihohi da suke fuskantar irin wannan bala’ai suna jihar su, sun kawo jiragen sama, mai saukar ungulu da jiragen ruwa da abinci da magani don ceto al’umar su.
Ya kamata majlisa tayi aikin ta na tsige gwamna Badaru domin yayi watsi da Jigawa, wanda wannan karara karya rantsuwar da yayi ne na shugabantar mutanen Jigawa.
Allah ya kasa muyi nasara a kan wannan jarabawa da take addabar mu.
alhajilallah@gmail.com
Discussion about this post