Tsohuwar mummunar gabar da aka yi a 2015 tsakanin ko kuma tun a 2014, tsakanin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas da tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, ta dawo ɗanya jagef.
Gaba ta shiga tsakanin su tun lokacin da Amaechi na Gwamna a jihar Ribas a ƙarƙashin PDP.
Abokan gabar su biyu dai duk ‘yan ƙabilar Ikwere ne, kuma lokacin da Amaechi ke gwamna, Wike ya yi masa Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jiha. Daga baya ya miƙa sunan sa Goodluck Jonathan ya naɗa shi Ƙaramin Ministan Ilmi a ƙarƙashin Minista Farfesa Ruqayyatu.
Gaba ta shiga tsakanin su daga lokacin da Amaechi ya fice daga PDP, ya koma APC, inda shi kuma Wike ya yi zaman sa a PDP, kuma ya tsaya takarar gwamna a 2015.
Amaechi ya tsayar da Dakuku Peterside ɗan takarar gwamna a APC, amma bai yi nasara ba. Shi kuma Wike ya yi nasara a 2015 da 2019.
A ranar Asabar ɗin nan ce Amaechi ya je ta’aziyyar Tonye Graham-Douglas, ɗan jihar wanda ya taɓa yin Minista sau biyu, a zamanin mulkin soja da mulkin farar hula.
A wurin ta’aziyya sai Amaechi ya ragargaji gwamnatin Wike saboda ta ƙi ɗaukar nauyin bikin rufe gawar Graham-Douglas.
“Idan aka dubi irin gagarimar gudummawar da marigayi Graham-Douglas ya bayar a Jihar Ribas da ƙasa baki ɗaya, abin takaici ne a ce Gwamnatin Jihar Ribas ba ta karɓi bikin rufe gawar sa ba, kuma ba ta karrama shi ba.” Inji Amaechi.
Sai dai kuma kwana biyu bayan nan, Wike ya ragargaji Amaechi a wurin wani taron buɗe ayyukan ci gaba da ya yi.
“Tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ba shi da kunya. Ya je ta’aziyya ya na cewa wai ba mu yi wa Graham-Douglas komai na ƙoƙari ba.
“To Amaechi ya je ya tambaya, mun yi iyakar ƙoƙarin mu domin su ga ya rayu. Abin da gwamanti ta kashe masa bai gaza ga naira miliyan 50 ba.
“Shi kuma Amaechi na can ya na gallafiri, bai tuna da Graham-Douglas ba lokacin da ya ke fama da rashin lafiya, sai bayan ya mutu zai zo saboda ba shi da kunya, har ya riƙa surutun wai ba mu rungumi bikin rufe gawar Graham-Douglas ba.
“To ya sani mun janye daga taron rufe shi ne, saboda mun ga an shigo da siyasa a wurin rufe gawar.
“Don haka Amaechi borin-kunya ne kawai ya ke yi, saboda bai tsinana wa jihar Ribas komai ba. Saboda haka ya yi wa mutane shiru.” Inji Amaechi.
Discussion about this post