A daidai ana shirye-shiryen fara kamfen domin zaɓen 2023, jam’iyyar APC na daɗa samun karuwa mai tsoka da mai a jihar Jihar Kaduna.
Ranar Litinin wasu dandazon ƴan jam’iyyar PDP suka tsunduma APC domin a haɗa hannu da su wajen kayar da tsohuwar PDP a jihar.
Ƴan PDP ɗin da suka sauya sheka daga shiyyar Kaduna ta tsakiya, sun kai wa ɗan takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya na APC, Muhammad Sani Dattijo ziyara domin nuna goyon bayan su ga tafiyar sa.
A jawabin da yayi a wajen bikin wankan sabbin ƴan APC ɗin, jagorar tafiyar, tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna, Abdulrasheed Kankanba, ya ce ” Mun kawo maka ziyara ne domin mu nuna maka goyon bayan mu ga takarar ka da kuma tabbatar maka cewa zamu yi maka aiki da jam’iyyar APC tuƙuru domin samun nasarar ta.
A jawabin sa, ɗan takarar sanatan Kaduna ta tsakiya, Dattijo, ya godewa tawagar gabaɗayan su da kuma yi musu alkawarin jam’iyyar za ta yi tafiya da su duk da cewa su sabbin shiga.
” Tare za mu yi tafiya da ku, ba za mu nuna banbancin don kuna sabbin shiga ba. Sannan kuma ina matukar farinciki da wannan shawara da kuka ɗauka na shiga jam’iyyar mu, da fatan tare duka za mu kai ga nasara, in Allah ya yarda.
Tsohon kakakin gwamnan Kaduna, Ahmed Maiyaki na daga cikin waɗanda suka amshi bakin tare da Dattijo a garin Kaduna.
Discussion about this post