Fitaccen malamin addinin musulunci dake garin Kaduna, Sheikh Gumi ya yi tir da farmakin da jami’an hukumar tsaro ta SSS suka kai gida da ofishin Tukur Mamu a Kaduna.
Gumi ya nuna fushin sa bisa tsare Mamau da jami’an SSS suka yi a lokacin da yake sharhi a wajen karatu da tayi ranar Asabar.
” Idan aka kama mutum, kotu yakamata a kai shi ba a tsare shi ba ya wuce awa 24. Yin haka shima ‘Ta’addanci ne’. Muna yaki da ƴan ta’adda saboda sun karya doka, idan gwamnati ta karya doka ita ma ta zama ƴar ta’adda.
” Na san yadda jami’an tsaro kan tilasta mutum yayi abinda ba haka, ko su kantara masa karyar da bai ji ba bai gani ba, ni ma tsohon jami’in tsaro ne, saboda haka na san yadda wasu jami’an tsaron suke. A kaishi kotu tunda wuri domin haka yake a dokar kasa.
A karshe Gumi yayi kira ga hukumar SSS su gaggauta kai Mamu kotu domin haka doka ya ce.
Dalilin da ya sa SSS ta kai farmaki gida da ofishin Tukur Mamu a Kaduna
Jami’an SSS sun kai farmaki gida da Ofishin Tukur Mamu dake jihar Kaduna ranar Alhamis bayan sun yi awon gaba da shi a filin jirgin saman Aminu Kano ranar Laraba.
Mamu wanda shi ne mawallafin jaridar Desert Herald, ya kasance mai sasantawa da shiga tsakanin ‘yan ta’adda wanda hakan ya sa aka sakin wasu fasinjojin da ‘yan ta’adda su ka kama tun cikin watan Maris, 2022.
Yan Sandan Ƙasa-da-ƙasa (Interpol) sun damƙe Tukur Mamu a filin jirgin saman Cairo na ƙasar Masar.
An kama Mamu a lokacin da ya ke jiran wani jirgi wanda zai shiga zuwa Saudi Arabiya daga Cairo, babban birnin ƙasar Masar.
Wata majiya Kuma makusancin iyalin Mamu ta bayyan wa PREMIUM TIMES cewa jami’an SSS sun kawo farmaki gidan sa da misalin karfe 12:30 na safiyar Alhamis.
Majiyar ta ce jami’an SSS sun kwace wayoyin salula da komfutoci daga ofishin da gidan Mamu.
An kama Mamu tare da matan sa biyu, dansa Ibrahim da wani sirikinsa Faisal.
Jami’an SSS sun saki matan Mamu amma suna tsare da Ibrahim da sirikinsa Faisal.
Mamu dai a baya ya ce ya daina shiga tsakani ‘yan ta’adda domin a saki waɗanda aka yi garkuwa da su, tun bayan da ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya na yi wa rayuwar sa barazana.
Har yanzu dai akwai sauran fasinjojin jirgin ƙasa a hannun ‘yan ta’addar da su ka yi garkuwa da sama da mutum 64 a lokacin.
Discussion about this post