Ana ci gaba da jefa wa ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, Bola Tinubu majaujawar taɗiye shi, inda har ta kai shi ga fitowa fili ya nesanta kan sa daga zargin mallakar wasu manyan kadarori a ƙasar nan.
Cikin kadarorin da Tinubu ya nesanta kan sa da su sun haɗa da katafaren otal na zamani, Oriental Hotel da Civic Center da ke sabuwar unguwar hamshaƙan masu tashen kuɗi, Lekki Corridor, Legas.
Cikin wani bayani da ya ƙunshi nasarorin da Bola Tinubu ya samar a shekaru takwas da ya yi Gwamnan Legas daga 1999 zuwa 2007, Tinubu ya ce shi dai a lokacin da ya na gwamna ya samar wa ɗimbin masu zuba jari yanayin zuba jarin su wajen kafa wuraren samar wa ɗimbin jama’a ci gaba, musamman a Lekki.
“Lokacin ina gwamna wurin tsibin bola ce mai faɗin gaske iyakar ganin idon mutum. Sai da gwamnatin Legas ta shafe watanni kafin a kwashe bolar, wadda yanzu wurin ya zama birni an samu ci gaba kuma dubban jama’a sun samu aiki da muhalli da kuma wurin hada-hada.”
Hadimin Yaɗa Labaran Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas mai suna Jubril Gawat ne ya fitar da kwafen bayanan ci gaban wanda Tinubu ya yi bayanin.
Hotel ɗin Oriental dai an gina shi ne a kan titin Ozumba Mbadiwe a unguwar Victoria Island.
Lokacin da aka yi tarzomar #EndSARS hasalallu sun nemi ƙona shi, amma wani kamfani mai suna Western Media Product Company ya fito ya ce hotel ɗin sa ne, ba na Tinubu ba.
Shugaban kamfanin Taiwo Ali ya ce kashi 99% na hannun jarin kamfanin na sa ne, ko sisi babu na Tinubu a ciki.
Tinubu ya ce wurare irin su boat club da Civic Center da wasu da dama da ake dangantawa da shi, duk ba shi da ko sisi a ciki.
Discussion about this post