Karin maganar da Hausawa ke cewa, “gwano ba ya jin warin jikin sa”, ta yi daidai da jawabin da Buhari ya yi wa shugabannin duniya a Majalisar Ɗinkin Duniya. A jawwbin, Buhari ya nuna irin yadda gwamnatin sa ke bai wa ɗan Adam ‘yanci ta kowane fanni, tare da yin kira kan adalci.
A jawabin sa na ƙarshe a Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) wurin taro na 77, ya ce babban ma’aunin ayyukan da ya yi a ƙasa tun daga farko shi ma mutunta haƙƙin ɗan Adam, wanzar da aldaci a ƙasa da duniya gaba ɗaya.
“Bari na isar da bayani na na ƙarshe a kan wannan mimbarin. Shekarun da na shafe ina bauta wa ƙasa ta a ayyukan da na yi daban-daban, na koyi darasin wanzar da aldaci, mutumtaka da aiki da gaskiya a ciki da wajen Najeriya,” inji Buhari.
Sai dai kuma saɓanin abin da ya bayyana, sai dai kuma ayyuka da yawa waɗanda Buhari ya tafka na rashin adalci da take doka su na da yawa, tun daga 2015 da ya zama shugaban ƙasa zuwa yau.
Take Doka, Rashin Adalci Da Danne Haƙƙin Ɗan Adam A Mulkin Buhari:
Shugaba Buhari ya fara gwamnati cikin mummunan zubar da jinin ɗaruruwan mabiyan Shi’a a Zuriya, jihar Kaduna.
Watanni bakwai bayan rantsar da shi, Sojojin Najeriya sun buɗe wa ‘yan Shi’a masu tattali wuta cikin Disamba, a Zariya.
An zarge su da tare hanya su ka hana Babban Hafsan Sojojin Najeriya na lokacin, Tukur Buratai wucewa. An yini ana buɗe masu wuta, kuma aka je har gidan babban jagoran su Sheikh Ibrahim El-Zazzaky, aka buɗe masa wuta.
An kashe mutane fiye da 350, waɗanda Gwamantin Jihar Kaduna ta rufe su a cikin rami ɗaya. Cikin waɗanda aka kashe har da ‘ya’yan Zakzaky huɗu. Shi ma an ji masa ciwo shi da matar sa, kuma aka tsare shi. Sai cikin 2021 aka sake shi, aka hana su fasfo ballanata su fita waje neman magani.
Kotun Kaduna ce ta sallami Zakzaky kuma yawancin mabiyan sa da aka kama tun 2015, sai 2020 aka gama sakin su, bayan an kasa samun su da laifi.
A ɓangaren mabiyan sa dai sun ce waɗanda aka kashe za su kai mutum dubu ɗaya.
Har yau ba a gurfanar da ko soja ɗaya a kotu ba.
Tsare Omoyele Sowore Kan Zargin Yunƙurin Kifar Da Gwamnati (Revolution Now):
An tsare Mawallafin Shahara Reporters, Omoyele Sowore tun cikin Agusta 2019 a hannun DSS, inda a cikin Nuwamba a tuhume shi da yunƙurin kifar da gwamnati, inda ya shirya gagarimar zanga-zanga.
Duk da kotu ta riƙa bayar da umarnin a bayar da belin sa, gwamnatin tarayya ta yi wa kotu kunnen-uwar-shegu.
Bayan an bayar da belin sa cikin 2021, an hanaxshi fita daga Abuja da kuma Najeriya.
Kisan Mambobin IPOB, Lamarin Da Ya Haifar Da Rikicin Da Ake Fama Har Yau:
Cikin 2015 bayan Buhari ya hau mulki, sojoji sun kashe mambobin IPOB masu rajin neman kafa Biafra su 12 a Jihar Anambra. Wannan kisa ya jangwalo dagulewar tsaro a yankin, lamarin da har yau sai ƙara muni abin ke yi.
An kashe su ne lokacin da zu ke gangamin murnar kotu ta ce a saki jagoran su, Nnamdi Kanu.
Yanzu haka rikicin IPOB ya yi muni sosai, inda a jihohin Kudu maso Gabas su na kashe jami’an tsaro da lalata kadarorin gwamnati.
Jangwangwamar Fatali Da Umarnin Kotu Kan Sakin Sambo Dasuƙi:
Gwamnatin Buhari ta yi ƙaurin suna wajen take doka sosai, musamman dangane da tsarewar da SSS su ka yi wa tsohon Mashawarcin tsohon Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Sambo Dasuƙi.
Yayin da aka tsare shi shekaru kan zargin salwantar kuɗaɗen makamai, ba sau ɗaya ba, ba sai biyu ba kotu na bayar da umarnin a bada belin sa, amma gwamnati sai ta ƙi sakin sa. Sai daga ƙarshe aka sake shi, bayan ‘yan taratsi sun gaji da ragargazar gwamnati.
Yi Wa Sojoji Korar Tilas Daga Aiki:
CIkin 2016 Gwamnatin Buhari ta kori wasu zaƙaƙuran sojoji 38 ritayar dole. An kore su ba tare da an taɓa kama wa ɗayan su da laifi ba. Duk da an yi wa Buhari ƙorafin lamarin, ya yi kunnen-uwar-shegu, bai maida su ba.
Ɗaukar Jami’an SSS Aiki Ba Bisa Ƙa’ida Ba:
Cikin 2017 gwamnatin Buhari ta ɗauki jami’an SSS aiki ba bisa ƙa’ida ba.
An fallasa cewa a jihar Katsina kaɗai an dauki mutum 51, yayin da a Jihohin Kudu maso Kudu shida, aka ɗauki 42 kaɗai, jihohin Kudu maso Gabas biyar aka ɗauki mutum 50.
Duk da jama’a sun yi ta ƙorafi, gwamnatin Buhari ta yi masu kunnen-uwar-shegu. Kuma haka ya riƙa yi sau da dama a ƙorafe-ƙorafen jama’a, a wurare da dama da ake ganin gwamnati ta yi ba daidai ba.
Discussion about this post