Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang ya janye goyon bayan da ya ke yi wa dan takarar shugaban kasa na PDP.
Jang da wasu magoya bayan gwamnan jihar Ribas Nysome Wike sun fice daga kwamitin kamfen din Atiku saboda kin sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar PDP da shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya yi.
Sai dai kuma wata kungiya mai suna ‘Plateau for Atiku Group’ ta yi watsi da wannan sanarwa ta Jang, Shugaban ta Shedrack Best, ya ce basu tare da Jang, kuma bai yi shawara da su ba kafin ya fitar da sanarwar janye wa daga kwamitin kamfen din Atiku.
” Ina so in sanar wa duka ‘yan PDP cewa ba Jang bane shugaban jam’iyyar PDP a jihar Filato kuma ba mu tare da shi a wannan ra’ayi ta sa. mu dukkan mu a jihar Filato kuma ‘yan PDP muna yin Atiku, shi dai da ya ce ba zai yi ba mishi can” In ji Best.
A nashi martanin Kakakin Jang Clinton Garuba, ya bayyana cewa wannan kungiya na masoya Atiku, ba kungiya bace da aka santa, ” Wasu tsirarun muatne ne kawai suka tattara kansu wuri daya wai masoya Atiku. Abinda Jang yayi shine daidai kuma kowa na tare da shi.
” Ba mu hana su ci gaba da mara wa Atiku baya ba, anind muke kira akai shine kada su rika sa sunana Jang a cikin tarkacen su. Shi Jang yan tare ne da bangaren Wike kuma babu gudu ba ja da baya a tafiyar su na dole sai Ayu ya sauka daga kujerar shugaban jam’iyyar PDP.
Discussion about this post