Dakarun Najeriya dake aiki a karkashin ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe ƴan Boko Haram/ISWAP 250 a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan a cikin makonni biyu da suka wuce.
Darektan yada labarai na hukumar tsaron Najeriya manjo-janar Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja da yake bada bayanan nasarorin da dakarun suka yi a aikin samar da tsaro da suke yi ranar Alhamis.
Danmadami ya ce dakarun sun samu wannan nasara ne a dalilin kai wa ‘yan ta’addan hari da rundunar sojin sama da ƙasa da suka yi a kauyukan dake jihohin Borno da Yobe.
Ya ce a wani harin da dakarun suka kai sun kashe ‘yan ta’adda 52 sun kama wasu 14 tare sannan sun ceto wasu daliban Chibok da aka yi garkuwa da su masu suna, Jinkai Yama, Falmata Lawal da Asabe Ali.
Danmadami ya ce dakarun sun ceto matan Chibok din tare da ‘ya’yan su a wurare daban daban tare da wasu mutum 19 din da aka yi garkuwa da su.
“Jami’an tsaron sun kwato bama-bamai 3 bindigogi kirar AK-47 guda 12, FN guda uku, harsasai da dama.
“An sami bam Kiran AP mine guda daya, hasasai K 7.62mm gida 86, babur guda daya, kwari da baka 16, Keke 7 da wayar salula 10.
“Akalla Boko Haram /ISWAP da iyalan su 556 ne suka mika wuya cikinsu akwai maza 115, mata 189 da Yara 252.
Bayan haka Danmadami ya ce sojoji sun kama wani dake hada baki da Boko haram Mamuda Usman wanda aka fi sani da Bado a babban birnin tarayya Abuja.
Zuwa yanzu Usman na tsare a hannun jami’an tsaro.
Discussion about this post