Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na NNPP, Abba Kabir-Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-gida, ya ƙaryata ji-ta-ji-tar wai zai nemi gudummawar karo-karon kuɗin kamfen a wurin gangamin mabiya ɗariƙar siyasar Kwankwasiyya.
Ji-ta-ji-tar da ake watsawa a soshiyal midiya na cewa Abba zai nemi gudummawar naira 1,000 daga jama’a, domin ya tara kuɗin kamfen na zaɓen gwamna a 2023.
Kakakin Yaɗa Labaran Abba mai suna Sanusi Bature, ya bayyana cewa ƙarya ce da yarfen siyasa don kawai a ɓata kyakkyawan sunan da ɗan takarar NNPP ɗin ya yi.
Ya ce Gida-gida bai ƙirƙiro ko tunanin ƙirƙirar wata gidauniyar neman tara masa kuɗin kamfen ba.
“Mu na jan hankalin jama’a baki ɗaya, musamman al’ummar Jihar Kano kuma magoya bayan NNPP cewa su yi watsi da wani bidiyo da ake watsawa don a ɓata sunan ɗan takarar mu. ‘Yan adawa ne kawai su ka bijiro da shi don sharri da yarfen siyasa kawai.” Inji Bature.
“Mai girma na sane da gagarimar rawar da ABOKAN ABBA GIDA-GIDA da su ka kafa ƙungiya ke taka masa. Waɗanda abokan sa ne na cikin jami’o’i, manyan makarantu, ƙwararrun lauyoyi da masana shari’a, wasu daga cikin manyan ‘yan kasuwa. Sun haɗa kan su su na kishin kyakkyawar dimokraɗiyya, har su ka ga cancantar Abba Yusuf.
“Abba ya na sanar da cewa shi dai bai taɓa umartar shirya wata gidauniyar tara masa kuɗin kamfen ba don zaɓen 2023, wanda ba a ma kai ga farawa ba.
“Mu na kan bakan mu na jajircewa su ceto Jihar Kano daga mummunan hannun masu mulkin da su ka ƙanƙame su.” Inji sanarwar.
Abba Gida-gida zai fafata da
Mataimakin Gwamna Abdullahi Ganduje, wato Nasiru Gawuna wanda shi ne ɗan takarar APC na zwben gwamna a 2023.
Discussion about this post