Gwamna Nyesom Wike ya bayyana cewa shiga Abuja da ya yi a ranar Juma’a ya sa ya tuna ciwon kayar da shi zaɓen fidda gwani da ya ce an yi a PDP.
Wike ya bayyana haka a wurin ƙaddamar da wani littafi da Babban Mai Shari’a Audu Aboki na Kotun Ƙoli ya wallafa.
A wurin taron wanda Wike ne Babban Mai Ƙaddamarwa, ya ce bayan saukar sa filin jirgi, ya biyo ta jikin sitadiyan na ƙasa na Mashood Abiola, inda aka yi taron, amma ya na kallon wurin, sai ya tuna yadda ake yi masa tuggun da aka kayar da shi zaɓen fidda gwani, wanda Atiku Abubakar ya yi nasara.
“Ya Babban Mai Shari’a, na yi farin cikin gayyata ta wannan taro da ka yi. To amma kuma ban ji daɗin yadda na biyo ta jikin sitadiyan ɗin aka yi zaɓen fidda gwani ba. Saboda ina kallon wurin sai na tuna yadda aka ƙayar da ni zaɓen fidda-gwani a ranakun 28 da 29 ga Mayu, wanda abin ya yi mani ciwo.” Inji Wike.
Ya Babban Mai Shari’a, na so a ce ka kai wannan taron ƙaddamar da littafin ka a Legas ko Kano. Saboda ina shigowa Abuja, sai na ji duk an tayar min mikin haushin faɗuwa zaɓen da na yi.” Inji Wike a cikin raha da barkwanci.
“Rabon da na shigo Abuja tun washegarin kayar da ni zaɓen fidda gwani da aka yi a ranar 28 da 29 ga Mayu.
“Ni ba irin Gwamna Yahaya Bello na Kogi ba ne, wanda bayan an kayar da shi zaɓen fidda GWANI, ya ci gaba da karakaina a Abuja a kullum, bini-bini ya na Abuja.
Dangane da rikicin Wike da Atiku, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da wani jigon PDP ya ce Shugaban PDP Iyorchia Ayu ne janyo saɓani da Wike, domin bai kamata ya gidan gidan Tambuwal yin godiyar haɗa-bakin yin nasarar Atiku a zaɓen-fidda-gwani ba.
Wani jigon PDP kuma fitaccen lauya, Obunike Ohaegbu, ya bayyana cewa a gaskiya tun farko dai Shugaban PDP Iyorchia Ayu, ya tafka kuskure da ya je har gida ya yi wa Gwamna Aminu Tambuwal godiyar haɗa kai da ya yi da Atiku Abubakar aka kayar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a zaɓen fidda gwani.
Ohaegbu ya bayyana wannan ra’ayi na sa a cikin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talabijin na AIT, a ranar Alhamis.
Idan ba a manta ba, bayan Atiku ya yi nasarar kayar da sauran ‘yan takara, Shugaban PDP Ayu ya samu Tambuwal har Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto washegari, inda ya yi masa godiya, saboda ya ce dukkan magoya bayan sa su zaɓi Atiku.
An yi ittifaƙin cewa janyewar da Tambuwal ya yi ce ta sa Atiku ya samu yawan ƙuri’un da ya kayar da Wike.
Tun daga nan kuma Wike ya riƙa kiran su Tambuwal da Ayu maciya amana.
Sannan kuma kwana biyu bayan zaɓen fidda gwani, Wike ya ce janyewar da Tambuwal ya yi ba bisa ƙa’ida ya yi ta ba, ta zo a makare. Har ya ce “da na dama da na hargitsa taron zaɓen fidda gwanin PDP.” Inji Wike.
Tun daga ranar da Ayu ya kai wa Tambuwal ziyara, har yau jam’iyyar ba ta zauna lafiya ba.
Wike ya koma gefe tare da goyon bayan wasu gwamnonin PDP na kudu, su na neman a tsige Ayu domin a cewar da ya fito daga Arewa, yanki ɗaya da Atiku Abubakar.
Sai dai kuma yayin da ake ƙoƙarin sasantawa, yanzu kuma PDP ta naɗa Tambuwal Babban Daraktan Kamfen na yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar. Wannan lamari ko kaɗan ba zai yi wa Wike daɗi ba.
“Babban kuskure ne a nuno Ayu ya je godiya gidan Tambuwal, har ana watsawa a gidan talabijin da sauran kafafen soshiyal midiya.” Inji Ohaegbu.
Discussion about this post