Sanata Smart Adeyemi na APC daga Jihar Kogi ya nemi a kafa dokar da za ta haramta jam’iyyun siyasa tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakin takarar sa fitowa daga ɓangaren addini ɗaya.
Adeyemi na so a hana Musulmi da Musulmi ko Kirista da Kirista su fito takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa a lokaci ɗaya.
Ya yi wannan kira a ranar Lahadi, lokacin da ya kira taron manema labarai a Abuja.
Ya ce maganar gaskiya bayan zaɓen 2023 akwai buƙatar a kafa dokar hana ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa fitowa daga ɓangaren addini ɗaya.
Ƙudirin Adeyemi mai suna, “Ƙudirin neman yi wa dokar zaɓen 2022 garambawul da sauran batutuwan da su ka shafi zaɓe.”
Ya ce ya na so a cikin dokar a cusa cewa, “Babu wata jam’iyya da za ta tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakin sa daga ɓangaren addini ɗaya.”
Ya ce yin hakan zai kawo rage zaman ɗar-ɗar da kuma ƙara fahimtar bangarori na addinai da kuma kawo haɗin kan mabambanta addinai a ƙasar nan.
“Ni dai a matsayi na na ɗan Najeriya, haƙƙi na ne na sauke nauyin abin da ke cikin zuciya ta, watau na fito na faɗi gsskiya. Wanda kuma duk ya yi min wata fassara daban ko yarfen siyasa, to shi ya shafa.” Inji Adeyemi.
Ya ƙara da cewa shi dai a matsayin sa na Kirista, ya na goyon bayan matsayar da Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), inda ta ce ba ta yarda da Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a APC ba, saboda shi da Tinubu mai takarar shugaban ƙasa duk Musulmai ne.
Sai dai kuma duk da haka ya ce ya na goyon bayan takarar shugabancin da Tinubu da Shettima ke yi, saboda sun cancanta.
“Ni matsayi na daidai ya ke da matsayar CAN, amma hakan ba zai sa na ƙi goyon bayan Tinubu da Shettima su yi nasara ba.
Discussion about this post