Sakamakon ambaliyar ruwan da ta cika Kasuwar Kantin Kwari a Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje ya bada umarnin a rushe duk wani gini da aka yi kan hanyar babbar magudanar ruwa ta Kwarin Gogau da ke Fagge.
Haka kuma ya bada umarnin a gaggauta rushe duk wani gini a cikin Kasuwar Kantin Kwari, wanda aka yi a kan magudanun wura a cikin kasuwar.
Wannan umarni ya biyo ambaliyar da ta janyo asarar ɗimbin kayayyakin miliyoyin nairori a cikin kasuwar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ganawar sa da manema labarai a ranar Laraba.
An yi ganawar bayan kammala taron Majalisar Zartaswa ta jihar, inda aka cimma matsayar gaggauta yin rusau ɗin.
Dama kuma an naɗa kwamiti a ƙarƙashin Kwamishinan Ayyuka Idris Saleh da Kwamishinan Muhalli Kabiru Getso domin duba wuraren da su ka wajaba a rushe.
Za a kuma rushe duk wani ginin ‘tamforare’ da aka yi kan magudanun ruwa a cikin Kantin Kwari.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda ambaliya ta dagula unguwanni da Kantin Kwari a Kano.
Ruwan da aka sheƙa a ranar Lahadi da Litinin ya haifar da ambaliya mai yawan gaske a cikin Kano.
Wuraren da lamarin ya shafa su na da yawa, kama daga bakin Tashar Jiragen Ƙasa, titin Ƙofar Mazugal, Rijiyar Lemo, France Road da sauran wuraren da aƙalla sun fi 30.
Wanda ya fi yin ɓarna shi ne ambaliyar da aka yi a wasu layuka cikin Kasuwar Kantin Kwari.
Ruwa ya shiga kantinan da ke ƙasa masu yawan gaske. Kowane layi ruwa ne ya cika maƙil, har ta kai shugabannin kasuwa sun fito a cikin ruwan su na yin duba-garin irin ɓarnar da ibtila’in ruwan ya yi.
Haka nan kuma ruwan ya haifar da asara mai ɗimbin yawa ga masu kasa kaya kan hanya a cikin kasuwar.
Ɓarnar ambaliyar ta yi munin da har ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar naira miliyan 50 ga ‘yan kasuwar Kantin Kwari, waɗanda ambaliyar ta shafa.
Jaridar Solacebasehausa ce ta buga labarin bayar da gudummawar ta Atiku, kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Sanata Ibrahim Shekarau, Sule Ya’u Sule ya watsa labarin da jaridar ta buga.
Wakilin mu ya ga wani bidiyo da Gwamna Abdullahi Ganduje ya wuce ta wani titin da ruwa ya mamaye.
Mutane da yawa a cikin Kano da Kasuwar Kantin Kwari da wakilin mu ya zanta da su ta waya, sun shaida masa cewa ambaliyar da ake fama ita a Kano matsala ce da Gwamantin Ganduje ta haifar.
Ana zargin Gwamnatin Ganduje ko kuma Gwamnan da kan da cewa ya kiɗime afujajan ya na sayar da filaye a ko’ina cikin Kano.
Kasuwar Kantin Kwari kuwa duk wanda ya santa a shekaru biyar baya, a yanzu idan ya shiga wurin ajiye mota ma gagara ya je yi, saboda duk wani fili an gine shi, an kuma gine wasu manyan layukan cikin kasuwar.
Gine-gine da su ka matse ya kawo ƙaranci da rashin wadatar magudanar ruwa a cikin kasuwar.
Haka nan kuma matsalar rashin bin tsarin gine-gine a cikin kasuwa ya kawo cunkushewar gine-gine da cinkoson jama’a a Kasuwar Kantin Kwari, wadda a yanzu ta cunkushe kamar Kasuwar Kofar Wambai, wadda motoci kan rasa ta inda za su ratsa su shiga.
A cikin unguwanni kuma da manyan titinan Kano, ambaliya ta yi ɓarna sosai, tare da kawo tsaikon zirga-zirgar ababen hawa a sassan da ambaliyar ruwan ya afku.
Discussion about this post