Bulalar Majalisar Dattawa, Orji Kalu ya bayyana cewa ƙabilar Igbo na su da wata damar yin shugabancin Najeriya a zaɓen 2022.
Ya ce tilas sai Igbo sun sake jira zuwa wani lokaci domin a ga “yadda ‘yan Najeriya za su miƙa karɓa-karɓar shugabancin Najeriya ga yankin Kudu maso Gabas.”
“Idan har za a naɗa wani ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa daga Kudu maso Gabas, to da ni ne zai samu. Amma kuma sai na fahimci a halin da ake ciki yanzu, lokacin samar da shugaban ƙasa ɗan ƙabilar Igbo bai yi ba tukunna.”
Kalu ya yi wannan bayani a Abuja ranar Talata, a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi.
Sanata Kalu ɗan ƙabilar Igbo ne, ya na cikin waɗanda su ka fara tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC. Sai dai kuma ya janye yayin da ya fahimci jam’iyyar ba za ta amince ta damƙa takarar shugabancin Najeriya zuwa yankin Kudu maso Gabas ba.
A kan haka ne sai ya bayyana sanarwar janye wa Sanata Ahmad Lawan, a bisa hujjar cewa shi ma ɗan yankin Lawal babu wanda aka taɓa zaɓe ya yi shugaban ƙasa daga Arewa maso Gabas. Lawan ɗan Jihar Yobe ne.
Kalu ya ce idan har Tinubu ya zama shugaban ƙasa, to ƙabilar Igbo su ne za su fi cin moriyar mulkin sa.
“Bari na faɗa maku gaskiya, ni da Tinubu mun yi gwamna a lokaci ɗaya. Ina Abiya ya na Legas. Mutum ne da ya iya tsara yadda za a kawo ci gaba da bunƙasa jama’a da ƙasa. Idan ya zama shugaban ƙasa, ƙabilar Igbo sai sun cin moriyar mulkin sa.” Inji Kalu.
Kalu ya ce a yanzu ba wai adawa ya ke yi da ɗan ƙabilar Igbo mai takarar shugaban ƙasa ba, kuma ba ya nukura idan ɗan ƙabilar Igbo ya zama shugaban ƙasa a yanzu.
“Amma dai ni ina ganin lokacin bai yi ba tukunna. Saboda idan mu na so mu yi shugabancin ƙasa, to tilas sai mun rungumi dukkan sauran al’ummar ƙasar nan. Saboda ƙarfe ɗaya ai ba ya yin amo.” Inji Kalu.
Kalu ya ce a yanzu shi dai ɗan jam’iyyar APC ne, kuma Bola Tinubu ne ɗan takarar su.
A yanzu dai Peter Obi ne mai ƙarfi daga cikin ‘yan ƙabilar Igbon da su ka fito neman shugaban ƙasa
Mafi yawan masu goyon bayan sa a yankin ƙabilar Igbo su ke.
Discussion about this post