Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Sam Obuabunwa, ya bayyana cewa abin da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ke yi a PDP daidai ne, domin so ya ke yi a yi adalci, ba wai tarwatsa jam’iyyar ya ke neman yi ba.
Ohuabunwa ya yi wannan bayani a wata tattaunawa da ya yi ranar Talata ɗin nan a gidan talabijin na Channels, a Abuja.
Ya ce Wike ya tabbatar ba a yi daidai ba, kuma kowa ya san ba a yi adalci wajen rabon muƙamai ba, an bayar da fifiko a wata shiyya, shi ya sa Wike ke son a gyara rashin adalcin da aka yi kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Ya ce shi da kan sa ya tuntuɓi ɓangaren Wike da ɓangaren Atiku, kuma an fahimci Wike ba son tarwatsa APC ya ke yi ba.
Ohuabunwa ya ce ganawar da Wike ya yi da Bola Tinubu ɗan takarar shugaban ƙasa na APC da wasu makusantan sa, ba alama ba ce mai nuna Wike na son fita ko zai fice daga PDP.
Yayin da rikicin Wike da Atiku da kuma Ayu ke ƙara muni, Rundunar Kamfen ɗin Atiku ta bayyana dalilin da ya sa ba za a iya cire Iyorchia Ayu ba.
Rundunar Kamfen ɗin takarar shugaban ƙasa ta Atiku Abubakar a PDP, ta bayyana cewa a halin yanzu ba zai yiwu a cire Iyorchia Ayu daga shugabancin PDP na ƙasa ba.
Ɗaya daga cikin Kakakin Kamfen ɗin Atiku mai suna Charles Aniagwu ya ce maimakon a cire Ayu daga shugabanci, ya ce PDP na ƙoƙarin neman wata mafita daban domin sasanta rigimar.
Ya ce PDP na duba wasu hanyoyi waɗanda doka ta tanadar a cikin dokokin jam’iyyar PDP.
Da ya ke magana da gidan talabijin na Arise TV ranar Asabar, ya ce cire Ayu zai kawo yi wa doka karan-tsaye a cikin jam’iyya, wanda hakan kuwa ka iya haifar da babban rikicin da ya dame wanda jam’iyyar ke fama da shi ya shanye.
Ya ce rikicin da ake yi dalilin ɓangaren Gwamna Nyesom Wike na neman a cire Ayu, to a yanzu dai ba zai ciru ba, saboda Kwamitin Zartaswar PDP ya jaddada gamsuwa da yarda da shugabancin sa.
Ya ce akwai wani hurumi a cikin kundin dokar PDP na 2017 wanda bai yiwuwa a saɓa masa.
“Dokar PDP ta 2017 ta ce tilas Mataimakin Shugaban Jam’iyya wanda idan babu shugaba shi ne zai maye gurbin sa, to ya kasance ya fito shiyya ɗaya tare da shugaban jam’iyyar.”
“Na uku da zai iya riƙe shugabancin jam’iyya idan aka cire shugaba kafin a yi wani zaɓe shi ne Sakataren Jam’iyya.
“Sashe na 45 ya ce idan babu shugaba to mataimakin sa ne zai zama shugaban riƙo kafin a sake zaɓe, ko kuma kafin a yi taron Majalisar Zartaswar PDP inda za a gyara tsarin Shugabancin Jam’iyya.”
Aniagwu ya ce kai ko da a yanzu Ayu ya sauka don ɗan kudu ya zama shugaban jam’iyya, to tilas sai an karya dokar jam’iyyyar PDP kenan.
“Za a iya cire Ayu kam, amma fa tilas sai idan za a haɗa har da Mataimakin Shugaba duk a cire su.
“To kuma idan an cire shugaba da mataimakin sa daga Arewa, aka maye gurbin su da ‘yan Kudu, to kuma ai na uku a muƙamin shugaban jam’iyya, wato sakatare, ai shi kuma ɗan Kudu ne daga jihar Imo, waro Sanata Samuel Anyanwu.
“Shin idan kun ce a maida muƙamin shugaba da mataimakin sa zuwa kudu, kun yarda a maido muƙamin sakatare daga kudu zuwa Arewa kenan?
Ya ce shi ya sa ake ganin babu zancen saukar Ayu, domin saukar sa zai haifar da rikici cikin jam’iyyya, wanda APC ke ta jiran ya faru a PDP.
Ya ce shi ya sa don a haƙura a samu a yi zaɓe, tunda saura watanni shida zaɓe kawai. Kuma dalili kenan Walid Jibrin ya sauka daga muƙamin Shugaban Kwamitin Amintattu, aka naɗa Alphonsus Wabara daga Kudu.
Discussion about this post