Wani jigon PDP kuma fitaccen lauya, Obunike Ohaegbu, ya bayyana cewa a gaskiya tun farko dai Shugaban PDP Iyorchia Ayu, ya tafka kuskure da ya je har gida ya yi wa Gwamna Aminu Tambuwal godiyar haɗa kai da ya yi da Atiku Abubakar aka kayar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a zaɓen fidda gwani.
Ohaegbu ya bayyana wannan ra’ayi na sa a cikin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talabijin na AIT, a ranar Alhamis.
Idan ba a manta ba, bayan Atiku ya yi nasarar kayar da sauran ‘yan takara, Shugaban PDP Ayu ya samu Tambuwal har Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto washegari, inda ya yi masa godiya, saboda ya ce dukkan magoya bayan sa su zaɓi Atiku.
An yi ittifaƙin cewa janyewar da Tambuwal ya yi ce ta sa Atiku ya samu yawan ƙuri’un da ya kayar da Wike.
Tun daga nan kuma Wike ya riƙa kiran su Tambuwal da Ayu maciya amana.
Sannan kuma kwana biyu bayan zaɓen fidda gwani, Wike ya ce janyewar da Tambuwal ya yi ba bisa ƙa’ida ya yi ta ba, ta zo a makare. Har ya ce “da na dama da na hargitsa taron zaɓen fidda gwanin PDP.” Inji Wike.
Tun daga ranar da Ayu ya kai wa Tambuwal ziyara, har yau jam’iyyar ba ta zauna lafiya ba.
Wike ya koma gefe tare da goyon bayan wasu gwamnonin PDP na kudu, su na neman a tsige Ayu domin a cewar da ya fito daga Arewa, yanki ɗaya da Atiku Abubakar.
Sai dai kuma yayin da ake ƙoƙarin sasantawa, yanzu kuma PDP ta naɗa Tambuwal Babban Daraktan Kamfen na yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar. Wannan lamari ko kaɗan ba zai yi wa Wike daɗi ba.
“Babban kuskure ne a nuno Ayu ya je godiya gidan Tambuwal, har ana watsawa a gidan talabijin da sauran kafafen soshiyal midiya.” Inji Ohaegbu.
Discussion about this post