Tsohon Gwamnan Jihar Filato Jona Jang, ya bayyana cewa ba wasu su ka haddasa ruɗani a cikin PDP ba, sai Shugaban PDP Iyorchia Ayu da Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto.
Jang ya ce su ne tun ma kafin lokacin zaɓen fidda-gwani a ranakun 28 da 29 Ga Mayu, su ka shirya tuggun da aka kayar da Gwamna Nyesom Wike na Ribas da sauran ‘yan takara.
Jang ya Yi wannan iƙirarin ne bayan magoya bayan ɓangaren Wike sun tashi daga taron ɓalle wa daga kwamitin kamfen ɗin Atiku.
Sun yi taron a gidan Wike, cikin Fatakwal. Bayan tashi taron dai sun bayyana janyewa daga kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku 2023.
Janga a ce Ayu a matsayin sa na shugaba, ya nuna son rai da goyon bayan wani ɗan takarar zaɓen fidda gwani.
Jang ya ƙara da cewa, a lokacin zaɓen Ayu a matsayin sa na alƙalin wasa, ya nuna goyon bayan ɓangaren Atiku Abubakar, inda ya haɗa baki da Tambuwal su ka shirya wa Wike da sauran ‘yan takara tuggu.
Haka kuma ya ce ba daidai ba ne da Ayu ya riƙa zumuɗin gode wa Tambuwal da kuma kai masa ziyarar godiya har gida da ya yi, bayan kammala zaɓen.
Wannan jarida ta buga raddin da Atiku ya yi wa Wike bayan ya samu labarin cewa Bataliyar Wike ɗin ta janye daga Rundunar Mayaƙan PDP 2023.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya yi mamaki sosai, jin cewa Gwamna Nyesom Wike na Ribas da tawagar sa sun janye daga kwamitin yaƙin neman zaɓen ATIKU 2023.
Cikin wata sanarwa daga Atiku, ya ce yayin da abin da Wike da tawagar sa su ka yi ya ba shi mamaki sosai, a gefe ɗaya kuma ya ce shi a kankin kan sa ba zai iya tilasta wa Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka ba, har sai idan shi Ayu ɗin ne da kan sa ya saura don ra’ayin kan sa.
Atiku ya ce bai yiwuwa a tilasta wa Ayu sauka, kamar yadda ɓangaren Wike ya jajirce sai an yi, sai fa ta hanyar da dokar ƙasa da dokar jam’iyyyar PDP ta tanadar.
Dangane da janyewar su kuwa, Atiku ya ce ya yi mamaki, domin in banda ‘yan kwamitin da aka zaɓa daga Jihar Ribas, na sauran jihohin da su ka goyi bayan Wike, duk uwar jam’iyya ta jihohin su ce ta gabatar da sunayen su.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Bataliyar Wike ta janye daga Rundunar Yaƙin Atiku 2023.
Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar 2023 ta afka cikin ruɗani, yayin da bataliyar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ke jagoranta ta janye jiki daga shiga yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ɗin.
Wannan janyewar da su ka yi ta zo ne daidai saura mako ɗaya a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, wanda INEC ta bayar da iznin fara fafatawa daga ranar 28 ga Satumba.
Sanarwar ta fito ne daga bakin ɗaya daga cikin zaratan Wike, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Olabode George.
Bode George ya yi sanarwar bayan sun kwashe tsawon ranar Talata zuwa washegarin Laraba su na ganawar sirri a gidan Gwamna Wike da Fatakwal.
Daga cikin mayaƙan da su ka halarci taron janyewa daga rundunar Atiku 2023, akwai Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, Olabode George, tsoffin gwamnoni irin su Segun Mimiko, Ayo Fayose, Donald Duke, Ibrahim Ɗanƙwambo, Jonah Jang da tsohon Ministan Shari’a, Mohammed Adoke.
Akwai kuma tsohon Minista Jerry Gana da Shugaban PDP na yankin Kudu maso Kudu, Dan Orbih, sai tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, Chibudom Nwuche da wasu hamshaƙan PDP da dama.
Ɓangaren Wike ya ce ba zai shiga kamfen ɗin Atiku ha har sai Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙamin sa, an naɗa ɗan Kudu, domin a yi adalcin raba-daidai.
Wani jigon PDP dai ya ce tun farko Ayu ne janyo saɓani da Wike, domin bai kamata ya gidan gidan Tambuwal yin godiyar haɗa-bakin yin nasarar Atiku a zaɓen-fidda-gwani ba.
Discussion about this post