Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya yi watsi da surutan da ake yi cewa ya dawo daga rakiyar Gwamna Nyesom Wike na Ribas.
Da ya ke magana da manema labarai, jim kaɗan bayan dawowar sa daga Landan, Ortom ya ce har yau har gobe ya na bayan Wike, kuma zai ci gaba da yaƙar rashin adalcin da aka yi masa a zaɓen fidda gwani.
Wasu kafafen yaɗa labarai sun buga cewa Ortom ya watsar da Wike, ya shiga rundunar kamfen ɗin Atiku Abubakar ɗan takarar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Amma da ya ke magana a ranar Talata, ya ce rahotannin da aka watsa aka ce ya rabu da Wike, sharri ne kawai da ƙarairayi.
Ya ce an ƙirƙiri labarin ne kawai domin a ƙara rura wutar rikicin PDP, sannan kuma ya ƙaƙaba husuma tsakanin sa da Wike da sauran gungun magoya bayan Wike.
Sannan Kakakin Yaɗa Labaran Ortom, mai suna Nathaniel Ikyur, ya ruwaito cewa, “babu saɓani ko bijirewa tsakanin gungun su Wike da ni. Har har yanzu ina goyon bayan Wike dangane da rashin adalcin da aka yi masa shi da guruf ɗin mu.
“Da safiyar Talata ɗin nan na dawo daga Landan tare da Wike, kuma har yanzu ina nan kan baka na da matsayar da na faɗa.
“An yi wa Wike rashin adalci. Kuma shugabannin jam’iyyar PDP su ka yi masa hakan, idan mai hankali ya yi la’akari da abin da ya faru lokacin zaɓen fidda-gwani.
“Sannan kuma har yanzu sun kasa yin abin da ya dace domin su warware matsalar su sasanta. Saboda haka ba zan daina goyon bayan Wike ba, har sai an yi masa adalci, an yi abin da ya dace a PDP daga can sama. Saboda ai har yanzu lokaci bai ƙure ba,” cewar Ortom.
Discussion about this post