Ofishin Kula Da Basussukan Da Ake Bin Najeriya (DMO) ya yi kira ga Majalisun Tarayya cewa su rage yawan giɓin da ake samu duk shekara a cikin kasafin kuɗi, domin a riƙa yawan bashin da Najeriya ke ciwowa a duk shekara.
Babban Daraktan DMO, Patience Oniha ce ta bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da bayanan a gaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe na Majalisar Tarayya.
Oniha wadda ta ce a yanzu bashin da ake bin Najeriya ya haura naira tiriliyan 40, ta ce a haka fa bashin zai ta ƙara yawa matsawar ‘Yan Majalisa su ka ci gaba da amincewa da kasafin kuɗi mai cike da giɓin da sai an ciwo basussuka za a iya cike su.
Oniha ta ce zunzurutun kuɗaɗen bashin da ake bin gwamnatin tarayya sun kai naira tiriliyan 41.6.
Ta ce bashin da ake bin Najeriya ya daɗa ƙaruwa ne sanadiyyar ɓarkewar cutar korona, inda daga lokacin zuwa yanzu aka ciwo bashin naira tiriliyan 9.
“A daidai Disamba 2020 bashin da ake bin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi naira tiriliyan 32.92 ne. Amma zuwa Disamba 2021 cikin shekara ɗaya bashin ya ƙaru zuwa naira tiriliyan 39.556. Zuwa Maris 2022 kuma yawan bashin ya ƙaru zuwa naira tiriliyan 41.6.
“Kuma kashi 85 bisa 100 na yawan waɗannan kuɗaɗen duk gwamnatin tarayya ake bashin su.” Inji Oniha.
“A duk shekara bashi na ƙaruwa saboda ku ne ke sa hannun amincewa kan kasafin kuɗi wanda sai an ciwo basussuka wasu ayyukan za su yiwu. Saboda haka kenan ku ne ke bada lasisin da Najeriya ke fita ta ciwo bashi kenan.” Inji ta.
Yayin da ke nanata cewa su riƙa tsefe gashin kan kasafin kuɗi a duk shekara kafin su kitse kan su damƙa wa Shugaban Ƙasa ya sa hannu, Oniha ta kuma bada shawara cewa a ƙara azamar samun hanyoyin ƙaruwar kuɗaɗen shiga a ƙasar nan.
Discussion about this post