Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ƙarin Kuɗaɗen Rangadin Ayyuka (DTA) ga Ministoci, Manyan Sakatarori da dukkan ma’aikatan gwamnatin tarayya, tun daga mataki na 1 zuwa na 17.
Wannan amincewar ƙarin kuɗaɗen alawus da aka yi masu ta na cikin wata takardar sanarwa da Shugaban Hukumar Tsara Albashin Ma’aikata Ekpo Nta ya fitar a ranar 31 Ga Agusta.
Sanarwar wadda aka raba ga dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya, ta ce ƙarin alawus ɗin zai fara aiki daga ranar 1 Ga Satumba.
“Shugaban Najeriya ya amince da ƙarin kuɗaɗen alawus ɗin rangadin aiki ga Manyan Sakatarori daga Naira 20,000 zuwa Naira 70,000. Su kuma Ministoci daga Naira 35,000 zuwa Naira 80,000”. Inji Shugaban.
“Duk wani mai neman wani ƙarin bayani to tuntuɓi wannan hukuma.”
Ƙarin Kowane Matakin Albashi:
GL 01-04 naira 10,000.
GL 05 – 06 naira 15,000.
GL 07 – 10 naira 17,500.
GL 12 – 13 naira 20,000.
GL 14 – 15 naira 25,000
GL 16 -17 naira 37,500.
Manyan Sakatarori Da Ire-iren Su – Naira 70,000.
Ministoci/Sakataren Gwamnatin Tarayya/Shugaban Ma’aikata Naira 80,000.
Wannan ƙari ya bai wa ‘yan Najeriya mamaki ganin cewa an yi ne daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsanancin rashin kuɗi da kuma ɗimbin bashin da ake bin ta.
Sannan kuma kasafin 2022 ya na da giɓi na naira tiriliyan 7. Kuma basussukan da ake biya kowane wata ya haura adadin kuɗaɗen shigar da Najeriya ke samu kowane wata.
Dama kuma ana kukan cewa albashi da sauran kuɗaɗen tafiyar da ofisoshin gwamnatin tarayya ke cinye yawancin kuɗaɗen shigar da gwamnati ke samu.
Discussion about this post