Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Lawal Babachir ya lashi takobin ganin bayan takarar Bola Tinubu da Kashim Shettima na jam’iyyar APC a zaben 2023.
A hira da yayi da Talabijin ɗin Arise ranar Laraba, wanda Trust ta buga, Babachir ya ce gaba ɗaya Kiristocin yankin Arewa ba za su zaɓi APC a zaɓen shugaban kasa ba.
” Mu na bin mutanen mu wato kiristocin yankin Arewa kaf muna musu huɗubar kada su kuskura su zaɓi takarar Muslim-Muslim, wato Tinubu da Shettima, kuma gaba ɗayan mu a yankin Arewa za mu kai su kasa.
” Tsayar da musulmi shugaban kasa, mataimaki musulmi, sheɗancin gaske ne, amma kuma za su kwashi kashin su a hannu, domin da ni da Yakubu Dogara da wasu gaggan kiristocin yankin Arewa muna aiki tukuru domin mu karya wannan tafiya na Muslim-Muslim, wato Tinubu da Shettima.
” Mu na bin duk wani mai faɗa a ji kirista a yankin Arewa da kungiyoyi da mutane, su tabbata sun yi katin zaɓe su kuma zauna da shiri. Sannan kuma muna tattaunawa da babban jam’iyya da muke ganin ita ce ke kan gaba domin mu haɗa hannu da su mu kada APC a zaɓen shugaban ƙasa.
Babachir ya kara da cewa idan suka yi rugurigu da APC a zaɓen shugaban kasa, nan gaba babu wani mutum ko jam’iyya da zai sake tunanin yin takara Muslim-Muslim.
Idan ba a manta ba, tun bayan bayyana Kashim Shettima da Bola Tinubu yayi a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban na APC Yakubu Dogara da Lawal Babachir suka lashi takobin ganin bayan wannan tafiya.
Su biyun duka sun lashi takobi ganin bayan wannan tafiya ta hanyar umartar kirisrocin yankin Arewa kaf kada su zaɓi jam’iyyar APC.
Discussion about this post