“Ba a kula masu kushe da hassada, Ba a yin la’akari da mai ƙoƙarin nuna gazawar mai ƙarfi,
Ko kuma masu ganin akwai inda mai yi masu ayyukan alheri ya kamata a ce ya fi haka ƙoƙartawa…”
-Theodore Roosevelt, tsohon shugaban Amurka
An shafe shekaru masu yawa, tun ma kafin samun ‘yancin Nijeriya, fitattun ‘yan jarida da mawallafa su na taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasar ƙasar nan. Sun tsunduma siyasa ne baya ga ayyukan sadaukarwar da su ka riƙa wa jama’a a gidajen jaridu. A duniya ma masu kafafen yaɗa labarai sun zama mashahuran shugabanni da manyan ‘yan siyasa.
Kafin ma a samu ‘yanci kafafen yaɗa labarai sun kasance masu bayar da gagarimar gudummawar neman ‘yanci. Kuma masu kafafen yaɗa labaran nan da ‘yan jaridu sun yi rawar gani sosai a manyan muƙaman siyasa. Kafin samun ‘yanci an samu bayyanar manyan masu damawa a harkokin jarida sun zama mashahuran ‘yan siyasa. Wato Sa Herbert Macaulay da Dakta Nnamdi Azikwe, wanda shi ne ya zama Shugaban Ƙasa na farko a ranar da Nijeriya ta samu ‘yanci, 1 ga Oktoba, 1960.
Fitattun ‘yan jarida da masu gidajen jaridu sun ci gaba da kutsawa cikin harkokin siyasa, tun daga wancan lokacin har zuwa yau, inda a Jamhuriya ta biyu aka samu biyu daga cikin su su yi nasarar zama gwamna. Cif Lateef Jakande ya zama Gwamnan Jihar Legas, shi kuma Segun Osoba ya zama Gwamnan Jihar Ogun.
Waɗansun su kuma da dama sun riƙe muƙamai daban-daban, tun daga ‘yan majalisa, ciyamomi da kansiloli, ko kuma shugabancin wasu hukumomi da cibiyoyi.
Cikin Oktoba 2019, mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya yanke shawarar shiga wancan daji na siyasa da manyan ‘yan jaridu da mawallafa su ka keta. Da ya shiga kuwa, ya fito gadan-gadan neman muƙamin siyasa.
Tun daga wancan lokaci ne kuwa tafiya mai nisan zangon watanni 31 ana tuntuɓar jama’a, ganawa, kamun-ƙafa da tattauna yadda za a kai ga cimma nasara.
Lokacin da Malagi ya fito, wasu mutane sun riƙa cewa ya dai fito kawai don ya tayar-da-ƙura. Wasu ma cewa su ke yi wasa ya ke yi kawai. Akwai kuma masu yi masa kallon mutumin da ya yi samun kuɗin da ake cewa ‘dare-ɗaya-Allah-kan-yi-Bature’, wanda ya rasa yadda kai kashe kuɗaɗen sa, ya shiga siyasa kawai don ya yi ɓarusa.
Akwai wasu da su ka riƙa yi masa kallon sabon-yanka-rake ne a siyasa, wanda a ganin su, bai isa ya yi gasa da tsoffin ‘yan alewar siyasa ba.
Dukkan waɗanda su ka riƙa tofa albarkacin bakin su dangane da shigar Malagi siyasa, sun yi tsammanin da ya fara, za a neme shi a rasa, wato zai yi tashin kumfar gishirin Andurus. Sun yi tsammanin ya shiga ne kawai don neman suna.
Dama haka aka riƙa yi masa irin wannan mummunar fassara, lokacin da ya fara wallafa jaridar Blueprint. Saboda ya shiga harkar da ƙarfin sa, har ya girgiza waɗanda su ka fara yi masa kallon raini a lokacin. To irin haka lamarin ya maimaita kan sa, lokacin da ya shiga siyasa, inda manyan masu ruwa da tsaki da masu ganin sai irin su wane da wane ke iya yin gwamna a Jihar Neja, su ka riƙa yi masa kallon sabon-shiga.
Malagi ya shafe watanni 30 ana gwagwagwa da shi, inda ya jajirce, ya nuna cewa shi fa ya kawo ƙarfi, don haka ya fi wane ya girme ni.
Daga lokacin da ya fara zuwa lokacin da ya fara shiga cikin zukatan jama’ar sa, Alhaji Mohammed Idris ya shimfiɗa hajar siyasar sa a farfajiyar Jihar Neja, inda ya riƙa shelar siyasar da babu tashe-tashen hankula, a gefe ɗaya kuma ya na kutsawa garuruwa da lunguna ya jaddada kamfen a bisa batutuwan da su ka shafi ci gaban jiha da al’ummar ta baki ɗaya.
Yayin da sauran ‘yan siyasa su ka maida hankali su na yarfe da bankaura ta hanyar amfani da soshiyal midiya, su ka riƙa raba kawunan jama’a, shi kuwa Alhaji Mohammed Idris Malagi ci gaba ya yi da yi wa jama’a albishir da muhimmancin haɗin kai domin a gina ƙasaitacciyar Jihar Neja.
Cikin wannan lokacin ya gana da masu ruwa da tsaki na kowace shiyya a jihar. Dalilin haka abin koyi hatta ga su kan su abokan adawar siyasa, waɗanda kafin shigar Malagi siyasa ba su iya zama inuwa ɗaya.
Malagi ya riƙa kai wa dattawan jiha ziyara, su da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da jagororin jama’ar yankunan karkara. Kuma ya jawo matasa, dattawa da maza da mata. Sannan ya riƙa yin la’akari sosai da masu ruwa da tsakin APC mai mulki a Jihar Neja.
Mohammed Idris ya yi amfani da kuɗaɗen sa, lokacin sa da tsarin tafiyar sa har ya yi nasarar ratsa zukatan ‘yan jam’iyyar APC reshen Jihar Neja. Ya taka rawa sosai wajen bai wa jam’iyyar gudummawa. Akwai lokacin da ya bayar da gudunmawar motoci 31 da naira miliyan 43.
Lokacin da ya ke yankar tikitin takarar gwamna, Malagi wanda a yanzu shi ne Kakaaki Nupe, ya nanata babban dalilin da na neman tsayawa takarar gwamna.
“Niyya ta domin ganin na ciyar da Jihar Neja gaba ta bunƙasa a fili ta ke. Idan na zama gwamna zan yi aiki tuƙuru, tun daga sa’ar farkon shiga ta ofis domin na zaƙulo zarata kuma ƙwararru daga mazaje, mata, matasa, masu ilmi da marasa ilmi, manoma, masu sana’o’in hannu, ‘yan tireda da kowa da kowa domin su bayar da gudunmawar da za su iya bayarwa.”
Tun daga lokacin da ya fara tuntuɓar jama’a, bai taɓa yarda zuciya ta ɗebe shi ya yi abin da ya saɓa wa kyawawan halaye da ɗabi’un sa ba.
Yayin da wasu ‘yan siyasar jihar su ka rungumi ‘yan daba, siyasar ƙiyayya, ramuwar-gayya da ɓata sunan abokin hamayya, shi kuwa Alhaji Mohammed Idris Malagi sai ya maida hankali wajen kamfen ɗin rashin tayar da hankula, haɗin kai da zaman lafiya. Sai da Malagi ya tuntuɓi dukkan ‘yan takarar gwamna a ƙarƙashin APC na Jihar Neja. Kuma irin wannan albishir ya riƙa yaɗawa a lokacin ganarwa sa ƙananan hukumomi da mazaɓun ‘yan majalisar tarayya na jiha.
A tafiye-tafiyen da ya yi tun daga Lapai zuwa Agaie, zuwa Bida, Kutigi da Borgu, har Kontagora da Minna, ya riƙa ganawa da sarakunan gargajiya, shugabannin karkara da ‘yan siyasa, bai taɓa yi wani furucin da zai harzuƙa wasu ko ya yi kalamin da zai rura wutar jituwa ba.
Kakaaki Nupe ya yi takara kuma an fafata da shi sosai. Lokacin da sakamakon zaɓen bai yi masa daɗi ba, tangarɗar rashin gudanar da zaɓen kamar yadda ƙa’ida ta gindiya bai hana shi fara taya murna ga wanda ya yi nasara ba. Ko bayan zaɓen fidda-gwanin an riƙa yi wa Malagi kallon da bai kamata ba a cikin jiga-jigan APC na jihar, amma ya dake tare da kai zuciya nesa.
Rashin nasarar da yi ba ta hana shi cika wa Kungiyar ‘Yan Jarida Reshen Jihar Neja (NUJ), alƙawarin motar da ya yi masu ba. A ziyarar godiya da su ka kai masa, ya ce shi ba shi da abokin gaba a ciki ko wajen siyasa.
Duk da an yi zaɓen fidda gwanin APC wanda aka yi hasashen shi ne zai yi nasara, amma hakan bai yiwu ba, a fili dai ta tabbata cewa bai yi nasara ba, amma kuma ya samu galabar riƙe alakar siyasa. Ya shiga tare da yin tasiri sosai a zukatan miliyoyin ‘yan Jihar Neja da sauran ‘yan Nijeriya masu cike da sanin cewa babban burin Malagi shi ne ya bunƙasa Jihar Neja.
Watanni uku bayan zaɓen fidda gwani, yanzu shi ne ya kasance abin kwatance a faɗin jihar. Kowa ya na nuna so da shauƙin yin kusanci da shi. Ana yi masa kallon sani sabon tauraron siyasar Jihar Neja, wanda duk sauran jam’iyyu ke ta shauƙin neman ya canja sheƙa, ya koma cikin su, su tsayar da shi takarar gwamna kawai.
Mohammed Idris mai shekaru 56 a duniya, mawallafin jarida ne kuma ƙwarraren massnin iya hulɗa da jama’a, yanzu ya zama wata rana ce da ta fito a siyasar Jihar Neja, wadda tafin hannu ba zai iya rufe ta ba. Ko ma dai me za a sake nanatawa dangane da sakamakon zaɓen fidda gwani da yadda aka gudanar da zaɓen, za a iya cewa an ɗauki ƙwaƙƙwaran darasi don gaba.
Jibrin Ndace ɗan jarida ne mazaunin Abuja.
Discussion about this post