Wata matar aure mai suna Florence Ideye ta roki kotun gargajiya dake Igando jihar Legas ta warware auren ta da mijinta Victor saboda malalaci ne ya yi shekara 10 baya aiki.
Florence ta ce ta gaji da zaman auren Victor saboda masifar sa, sannan kuma kullum sai dai ya kwanta bakinsa ya kafa karar sigari, gefen sa kuma kwalbar giya babu abin da ya dame shi.
Ta ce Victor ya daina aiki tun da wan sa ya rika aiko musu kudi suna cefane amma daga baya yayan nasa ya daina aiko masa da kudi shi kuma Victor ya ki komawa aiki.
“A da Victor makanike ne amma sai ya siyar da duk kayan aikinsa domin wai yanaso ya fita zuwa kasar waje.
“Tafiya zuwa kasar waje bai yiwu ba kuma ya ki komawa aikin sa na kanikan ci.
“Abin da ya fi kona mun rai shine yadda Victor ke aikar ‘ya’yan mu suna siyo masa kayan maye yana sha a gida.
“Tuni na tattara kayana na koma gidan iyaye na da zama saboda na gaji da zama tare da Victor.
Shikuwa Victor ya ce Florence na so ta rabu da shi saboda yanzu ta ga babu kudi.
Ya ce a lokacin da suka yi aure yana aikin tuka mota sannan naira 15,000 ne ake biyansa a wata amma sai wansa na aiko musu da kudi.
Alkalin kotun Adeniyi Koledoye ya daga shari’a zuwa ranar 11 ga Oktoba.
Discussion about this post