Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙalubalanci Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai, inda ta nemi ya bayyana sunayen sojojin da ya sun shaida masa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su daina kai wa ‘yan bindiga farmaki su na ragargazar su.
A cikin wata intabiyu da aka yi da Ortom ne dai ya yi iƙirarin cewa wasu manyan sojoji sun shaida masa cewa Buhari ya umarci a daina kai wa makiyaya ‘yan farmaki ana kashe su.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya ce iƙirarin Ortom tsagwaron ƙarya kawai, kuma ba yau ya fara shirya irin ta ba.
Daga nan sai Shehu ya ce idan abin da Ortom ya faɗa gaskiya ce, to ya fito ya bayyana sunayen jami’an sojojin da ya ce sun shaida masa haka ɗin mana.
Shehu ya ƙara da cewa a yanzu da guguwar zaɓe ta kunno kai, za a riƙa cin karo da irin ƙarairayin tayar da husuma irin waɗanda Ortom ke kantarawa.
“Maimakon dattijo kamar Ortom ya riƙa yin kalamai waɗanda za su kawo haɗin kai a cikin ƙasa, sai ya koma ya na ɓaɓatu irin na masu ƙoƙarin haddasa husuma.”
Ba wannan karon ba ne kaɗai da Ortom ya taɓa yi wa gwamnatin tarayya kakkausan zargi a bangaren tsaro.
Shehu ya ce Ortom na son yin amfani da siyasa a lokacin da ƙasar nan ke fama da matsalar tsaro domin ya yi tasiri.
Idan za a iya tunawa, Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ne ya yi kira ga sojoji cewa su lalubo hanyoyin magance matsalar tsaron Zamfara, ba tare da yin amfani da ƙarfin makamai ba.
Discussion about this post