Ɗan takarar gwamnan Jihar Enugu a ƙarƙashin APC, Uchenna Nnaji, ya fusata ya ƙi karɓar tallafin kuɗaɗen kamfen ɗin da Bola Tinubu mai takarar shugaban ƙasa a APC ya aika jihar.
Uchenna ya ƙi karɓar kuɗin bayan ya gano cewa saɓani ya shigo sosai a cikin APC a Jihar Enugu, kuma kuɗin ne ke neman raba jam’iyyar gida-gida.
Ya bayyana cewa ba zai karɓi kuɗaɗen Tinubu ba yayin da ya ke jawabi a wurin taron Shugabannin APC na tashen Kudu maso Gabas a Hedikwatar shiyya da ke Enugu.
“A bar kuɗin ba na so. Za mu yi amfani da kuɗaɗen da jam’iyya ke da su a Jihar Enugu mu yi kamfen. Bayan kamfen sai Tinubu ɗin ya biya mu kawai.”
Rikici ya ɓarke a cikin APC reshen Jihar Enugu, inda shugabannin jam’iyya ke cin karo da juna, kowa na cewa shi ke da haƙƙin raba kuɗaɗen da Tinubu ya aika masu wajen yin kamfen da sauran ayyukan jam’iyya.
Nnaji ya ce zai je ya samu Tinubu da Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu ya shaida masu dalilin da ya sa ya ce ba zai karɓi kuɗaɗen ba.
Daga nan ya ce ya kamata duk wasu masu zaman dirshan a Abuja da ke kiran kan su ‘yan APC na Enugu, su koma gida a yi kamfen domin a samu nasara a zaɓe mai zuwa.
Daga nan sai ya yi kira cewa kowa ya goyi bayan shugaban APC na Jihar Barno, Ugochukwu Agballah, wanda Nnaji ya ce shi ne ma ya farfaɗo da APC a jihar Enugu.
Ya ce ya karaɗe dukkan mazaɓun jihar guda 184, garuruwa 204 da ƙananan hukumomin jihar guda 17.
Discussion about this post