Kotun majistare dake Iyaganku a Ibadan jihar Oyo ta bada belin wani mai suna Sule Mosudi mai Shekaru 55 kan naira 50,000 dalilin kama shi da aka yi da laifin sace nonon ayaba a gonar da ba na shi ba.
Mosudi mazaunin kauyen Idi-Ayunre dake kisa da garin Ibadan ya saci ayaba a gonar wani Sikiru Oseni dake kauyen Abanla dake yanken Ibadan.
Farashin ayaban da Mosudi ya sata ya kai naira 4,000.
Lauyan da ya shigar da karar Foluke Oladosu ya ce Mosudi ya saci ayabar ranar 4 ga Satumba da misalin karfe ɗayan dare.
Oladosu ya ce mutanen unguwa sun kama Mosudi bayan ya saci ayaban saboda dokar hana walwala bayan karfe 11 na dare da aka saka.
A zaman da kotun ta yi a cikin wannan mako Mosudi ya musanta aikata haka.
Alkalin kotun I. O. Soho ya bada belin Mosudi akan naira 50,000 tare da gabatar da shaidu biyu.
Soho ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 10 ga Oktoba.
Discussion about this post