Jaridar Desert Herald ta yi karin bayani akan kayan sojojin da aka samu a gidan Tukur Mamu da ke tsare hannun hukumar SSS.
Manajan kamfanin Ibrahim Mada, ya bayyana cewa kayan da aka samu a gidan Mamu na ɗan ɗan uwan sa ne wanda yana aikin soja.
Binciken gidan Mamu
Hukumar tsaron sirri ta kasa SSS ta bayyana cewa ta samu tari kayan sojoji da maƙudan kuɗi jibge a gidan Tukur Mamu a Kaduna.
PREMIUM TIMES ta buga kama Mamu da jami’an SSS suka yi bayan saukar sa daga jirgin saman Egypt Air.
Jami’an tsaron Interpol na kasar Masar sun damke Tukur Mamu a filin jirgin saman kasar a hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya tare da iyalan sa.
Daga nan sai suka dawo da shi Najeriya inda jami’an SSS suka yi awon gaba da shi.
Bayan haka jami’an sun gudanar da bincike a gidan sa da ofishinsa da gidansa.
A sanarwar da hukumar ta fitar ranar Juma’ a, an samu kayan sojoji masu dinbin yawa a gidan Mamu sannan kuma da tarin kudi da suka haɗa da naira, daloli, Euro da Fan na kasar Ingila.
Tukur Mamu ne mai wallafin jaridar Desert Herald sanna kuma shine ke kan gaba wajen tattaunawa da ƴan bindiga wajen ceto waɗanda aka yi garkuwa da su musamman waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna.
Discussion about this post