Kakakin Yaɗa Labaran takarar shugaban ƙasa ta Bola Tinubu a APC, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Peter Obi tantirin maƙaryaci ne da ya ce Tinubu ba shi da ƙwarin jikin da zai iya shugabancin Najeriya.
Onanuga ya maida masa wannan raddi ne bayan Obi wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin LP ya yi iƙirarin cewa Tinubu ba shi da ƙoshin lafiyar da zai takarar shugaban ƙasa, ballanata shugabancin ƙasa.
Ya ce Tinubu garau ya ke, kuma a kullum ya na aiki sa’o’i 20 ya na kuma ganawa da mutane ana tattauna batutuwan yadda za a bunƙasa Najeriya.
“Banda ƙarairayi da shirme ai Peter Obi bai iya komai ba? Ta yaya kai da ba likitan mutum ba za ka iya iƙirarin cewa ba shi da lafiya.
Obi dai ya ce ko waɗanda ke kewaye da Tinubu sun san cewa ba shi da lafiya, “amma su na bin sane don kawai su samu kuɗi a jikin sa.”
Shi kuma Onanuga cewa ya yi kowa ya san Tinubu ne ya fi cancantar ceto Najeriya, saboda ya yi an gani a jihar Legas. “Shi kuma Peter Obi da ya yi gwamna bai tsinana komai ba sai burga da ƙarairayi kawai.
Peter Obi tun da farko ya zargi makusantan Tinubu cewa sun riƙa watsa bayanai a soshiyal midiya su na cewa kada a zaɓi Obi, domin idan aka zaɓe shi, “ƙabilar Igbo za su daina zuwa Legas, komawa za su yi gida su raya yankin Kudu maso Gabas.
Dama kuma kwana biyu da su ka gabata, Femi Fani-Kayode da Festus Keyamo sun maida wa Peter Obi raddin cewa Tinubu ba zai janye daga takarar 2023 ba.
Majalisar Kamfen ɗin Tinubu 2023 ta yi tofin Allah-wadai kan wani rahoto da ke yawo a soshiyal midiya mai nuna cewa wai Bola Tinubu zai janye daga takarar 2023, saboda rashin lafiyar da ke damun sa.
Cikin wata sanarwar da Femi Fani-Kayode, ɗaya daga cikin Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin TInubu 2023 ya fitar a ranar Litinin, ya ce rahoton labari ne na ƙarya, bogi ne, jabu ne wanda magoya bayan Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP su ka ƙirƙira, kuma su ka watsa.
Rundunar Kamfen ɗin TInubu ta ce ɗan takarar ta su garau ya ke, kuma gagau ya ke da ƙarfin sa. Kuma a cewar rundunar kamfen ɗin, Tinubu ya yi shiri tsaf domin jiran fara rangadin neman zaɓe don ya karaɗe ƙasar nan da kamfen.
“Mu na so mu yi amfani da wannan kafar yaɗa labarai don mu fito mu ƙaryata wani rahoton ƙarya, ƙage da sharri wanda magoya bayan Peter Obi su ka riƙa watsawa, mai ɗauke cda labarin cewa wai Asiwaju Bola Tinubu ya na shirin janyewa daga takara, bisa dalilai na rashin ƙoshin lafiya.
“Maƙaryata ne waɗannan masu kitsa wannan sharri, domin mu ɗan takarar mu lafiyar sa garau. Jira kawai ya ke yi a fara tantance fita kamfen domin ya karaɗe ƙasar nan ya na yaƙin neman zaɓe. Kuma ba da daɗewa ‘yan adawa za su fara jin rugugin muryar sa mai razana masu adawa da shi.”
Sannan kuma rundunar kamfen ɗin TInubu ta ƙaryata wani saƙon text wanda Peter Obi ya karanta a cikin taron jama’a.
Saƙon na ɗauke da sanarwar gargaɗi da jan-hankali ga jama’a, musamman ana cewa kada a zaɓi Peter Obi, zai kashe Legas da sauran johohin a raya yankin su na Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.
Wani Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen na Tinubu, wato Ƙaramin Minista Festus Keyamo, ya ce wannan yarfen ba daga wajen su ya fito ba.
Discussion about this post