Majalisar Kamfen ɗin Tinubu 2023 ta yi tofin Allah-wadai kan wani rahoto da ke yawo a soshiyal midiya mai nuna cewa wai Bola Tinubu zai janye daga takarar 2023, saboda rashin lafiyar da ke damun sa.
Cikin wata sanarwar da Femi Fani-Kayode, ɗaya daga cikin Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin Tinubu 2023 ya fitar a ranar Litinin, ya ce rahoton labari ne na ƙarya, bogi ne, jabu ne wanda magoya bayan Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP su ka ƙirƙira, kuma su ka watsa.
Rundunar Kamfen ɗin TInubu ta ce ɗan takarar ta su garau ya ke, kuma gagau ya ke da ƙarfin sa. Kuma a cewar rundunar kamfen ɗin, Tinubu ya yi shiri tsaf domin jiran fara rangadin neman zaɓe don ya karaɗe ƙasar nan da kamfen.
“Mu na so mu yi amfani da wannan kafar yaɗa labarai don mu fito mu ƙaryata wani rahoton ƙarya, ƙage da sharri wanda magoya bayan Peter Obi su ka riƙa watsawa, mai ɗauke cda labarin cewa wai Asiwaju Bola Tinubu ya na shirin janyewa daga takara, bisa dalilai na rashin ƙoshin lafiya.
“Maƙaryata ne waɗannan masu kitsa wannan sharri, domin mu ɗan takarar mu lafiyar sa garau. Jira kawai ya ke yi a fara tantance fita kamfen domin ya karaɗe ƙasar nan ya na yaƙin neman zaɓe. Kuma ba da daɗewa ‘yan adawa za su fara jin rugugin muryar sa mai razana masu adawa da shi.”
Sannan kuma rundunar kamfen ɗin TInubu ta ƙaryata wani saƙon text wanda Peter Obi ya karanta a cikin taron jama’a.
Saƙon na ɗauke da sanarwar gargaɗi da jan-hankali ga jama’a, musamman ana cewa kada a zaɓi Peter Obi, zai kashe Legas da sauran johohin a raya yankin su na Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.
Wani Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen na Tinubu, wato Ƙaramin Minista Festus Keyamo, ya ce wannan yarfen ba daga wajen su ya fito ba.
Discussion about this post