Ƴan ƙabilar Igbo mazauna jihar Kaduna sun gaba ɗayansu sun yi wa sanata Uba Sani, na jam’iyyar APC, kuma ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna mubaya’ cewa kaf din su a jigar shi za su yi.
Sanata Uba Sani ya kai ziyarar musamman ga shugabannin ƙabilar Igbo mazauna garin Kaduna ranar Talata.
A wurin taron shugabannin kungiyar, Ozo Chief Francis Nnaegbuna, Ozó Ndigbo da Chief Francis Ani gaba ɗayan su sun yabawa sanatan bisa karamci da ya nuna musu sannan sun yi masa alkawarin mara masa baya a zaben gwamna mai zuwa.
” Uba Sani na mu ne kuma muna tabbatar masa cewa lallai ƴan ƙabilar Igbo a Jihar kaf ɗin su shi za su dangwala wa kuri’a a zaɓen gwamna mai zuwa.
” Za mu sako sako, ƙurɗi-ƙurɗi domin jawo ra’ayin ƴan uwan mu su mara masa baya. Ba mu haufi ko tantamar cewa gaba ɗayannmu Inyamirai a jigar Kaduna Uba zamu zaɓa.
Dattijo Ozo Chief Francis Nnaegbuna, Ozó Ndigbo ya ba da tarihin zamantakewar sa da marigayi Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello a Kaduna da wasu manyan ƴan Arewa.
A karshe Sanata Uba ya gode wa shugabannin Inyamirai bisa karamci da suka nuna masa da goyon baya da suka yi alƙawarin bashi a zaɓe mai zuwa.
Sanata Uba Sani zai fafata da Honarabul Isah Ashiru na Jam’iyyar PDP, Jonathan Asake na LP, Hayatuddeen Lawal na PRP, Suleiman Hunkuyi na NNPP.
Discussion about this post