Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa ya haƙura da takarar sanatan da ya ke fafutikar neman sake tsayawa, tunda dai kotu ta kayar da shi.
Lawan ya ce ba zai ɗaukaka nasarar da Bashir Machina ya a kan sa, a Babbar Kotun Tarayya ta Damaturu ba.
Lawan ya rasa kujerar takarar Sanatan Yobe ta Arewa yayin da ya tafi neman takarar shugaban ƙasa a APC, inda bai samu damar yin zaɓen fidda gwani ba, kuma takarar shugaban ƙasa ɗin, can ma a ƙarshe ya janye ya bar wa Bola Tinubu.
Kotu Tarayya da ke Damaturu ta umarci INEC ta saka sunan Machina a matsayin halastaccen ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa.
Duk da cewa Machina ne ya ci zaɓen fidda-gwani, Sanata Lawan ya yi ta ƙoƙarin murɗe takarar ko ta halin ƙaƙa, bayan ya rasa kujerar takarar shugaban ƙasa.
Sai dai yanzu ya bayyana cewa ba zai ɗaukaka ƙara ba, ya rungumi ƙaddara, a cikin wata sanarwa da ya sa wa hannu da kan sa.
“Wannan hukunci da Kotun Tarayya ta yanke, ya haramta takarar da na nemi yi ta Sanatan Yobe ta Arewa.
“Bayan na yi tunani da tuntuɓar abokan siyasa ta da masu goyon baya na da masu yi min fatan alheri, na yanke shawarar cewa ba zan ɗaukaka ƙara ba.”
Lawan ya gode wa tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Gaidam da Gwamna Mai Mala-Buni.
Kuma ya yi godiya da fatan alheri ga ɗaukacin al’ummar mazaɓar sa, waɗanda ya ce zai ci gaba da yi masu duk abin da ya wajaba.
A na sa ɓangaren, lauyan Machina mai suna Ibrahim Bawa, ya jinjina wa alƙalin da ya yanke hukuncin bai wa Machina nasara kan Ahmad Lawan.
Ya ce lallai alƙalin ya yi “ƙarfin hali da ta-maza sosai.”
A wajen kotun ne ya ce lallai hukuncin da Mai Shari’a Fadima Aminu ta yanke ya ƙara wa ɓangaren Shari’a mutunci, karsashi da samun gaskatawa daga jama’a.
Discussion about this post