• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Ƴan ta’adda sun gamu da fushin sojojin Najeriya, sojoji sun kashe 50 sun kama 60

    GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA

    Yari ya raba tallafin tirela 145 cike maƙil da buhunan masara 145 ga mabuƙata a Zamfara

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

JAN AIKI A GABAN PDP: Wike, Saraki, Anyim sun ƙi halartar gayyatar da Atiku ya yi wa ‘yan takarar fidda-gwanin da ya kayar

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
September 8, 2022
in Babban Labari
0
MATAIMAKIN SHUGABAN ƘASA: Dalilin da ya sa Atiku ya ƙi ɗaukar Gwamna Wike

Yayin da saura makonni uku a fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa da na Sanatoci da Mambobin Tarayya, jam’iyyar PDP na ci gaba da nausawa cikin duhu, inda gaggan ‘yan takarar zaɓen fidda-gwanin da Atiku Abubakar ya kayar, su ka ƙaurace wa taron da ya kira su.

Daga cikin waɗanda ba su halarci taron na sirri wanda aka yi a gidan Atiku da ke Asokoro, Abuja ba, akwai Gwamna Nyesom Wike, na Jihar Ribas, Bukola Saraki kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Gwamna Udom na Akwa Ibom, Anyim Pius Anyim da wasu kuma.

Atiku dai ya kayar da ‘yan takara 13, kuma tun daga lokacin PDP ba ta sake zama lafiya ba, saboda Wike da magoya bayan sa gwamnoni sun ce sai dai Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayi ya sauka.

Waɗanda su ka halarci taron da Atiku sun haɗa da Shugaban Mujallar OVATION, Dele Momudu, Mohammed Hayatuddeeen, Tariela Oliver da kuma wasu daban.

Tufka Da Warwara:

Yayin da ake wannan taro a gidan Atiku, a Fatakwal kuwa Wike na can ya na buɗe katafaren tsangayar da ya gina a Jami’ar Fatakwal.

A wurin Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, ya shaida cewa su na nan kan bakan su, su na goyon bayan Wike cewa sai an saisaita rashin adalcin da aka yi masu a PDP idan ana so a tafi tare.

Cikin makon jiya dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga nazarin yadda rikicin Wike da Ayu ke dakushe wa Atiku ƙumbar yakushin manyan jam’iyyu.

Yayin da za a fara buga gangar kamfen ɗin zaɓen 2023 a ranar 28 Ga Satumba, 2022, rikicin da ya rincaɓe tsakanin Gwamna Nyesom Wike, Atiku Abubakar da Iyorchia Ayu na neman hana wa Atiku ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP kasa motsi mai ƙarfi.

Kwanaki kaɗan bayan taron sulhun da aka yi tsakanin Wike da Atiku a Landan, an yi tsammanin za a fara ganin canjin sassauci tsakanin ɓangarorin biyu.

Atiku ya shiga tsaka-mai-wuya a lokacin, domin ya na birnin Paris ya ji labarin cewa Wike ya gana da Tinubu da Obasanjo a Landan, daga can shi ma ya garzaya Landan ya yi zaman sasanci da Wike.

Sai dai kuma Wike da sauran gwamnonin da su ka take masa baya ganawar, su ƙeƙasa ƙasa sun ce sai Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya fara sauka an bai wa ɗan kudu riƙon-ƙwarya kafin su zauna sulhu tukunna.

Atiku ya ce zai duba buƙatun su tare da tuntuɓar manyan jam’iyya, lamarin da ba a san ranar da zai yi hakan ba. Duk da dai shugabannin jam’iyyar za su yi taro a ranar Alhamis, inda ake tsammanin za su cimma matsaya kan batun Ayu.

Tuni su dai ɓangaren Wike har sun nuna cewa Mataimakin Shugaban PDP na Shiyyar Kudu, Taofeek Arapaja su ke so ya zama shugaban riƙo kafin a shirya gangamin taron zaɓen wani shugaban.

Ana cikin wannan zaman zullumi, sai Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya fusata, ya ragargaji Wike da magoya bayan sa, inda ya kira su waɗanda “yarinta ke damun su.” Hakan kuwa ya ƙara dagula PDP sosai.

PREMIUM TIMES ta buga labarin da Ayu ya ce masu kiran na sauka daga shugabanci yarinta ke damun su.

Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa Iyorchia Ayu ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga shugabanci ba, saboda bai ga wani dalilin da zai sa a ya sauka ɗin ba.

Haka tsohon sanatan ya bayyana wa BBC Hausa a ranar Laraba.

Ayu na shan matsin-lamba daga ɓangaren Gwamna Nyesom Wike cewa saukar sa na daga cikin sharuɗɗan sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP.

Rundunar Wike ta jajirce cewa tilas sai Ayu ya sauka a naɗa wa PDP shugaban jam’iyya ɗan kudu, tunda Ayu da Atiku Abubakar duk ‘yan Arewa ne.

Gwamnonin kudu na PDP na ƙorafin yadda ba a yi rabon muƙamai na PDP bisa adalci ba.

Sannan kuma wasu shugabannin PDP na zargin Ayu da nuna goyon baya ƙarara ga Atiku Abubakar a lokacin zaɓen fidda-gwani.

Sai dai kuma a ranar Laraba Ayu ya ce masu kiran ya sauka yara ne a cikin jam’iyya, ba su ma san yadda aka kafa PDP ba.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda taron neman sulhu ya wakana tsakanin Wike da Atiku, kwanan baya a birnin Landan.

Martanin Ayu:

Ya ce an zaɓe shi ne fa a ƙarƙashin ƙa’idoji da sharuɗɗan da jam’iyyar PDP ta gindaya.

“Shugabannin jam’iyya kafin zaɓen shugaba sun ce babu ruwan su da yin la’akari da inda shugaban jam’iyya ya fito idan an zo zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar shugaban ƙasa.

“An zaɓe ni na yi shugabancin shekaru huɗu, kuma ban ma cika ko da shekara ɗaya a ofis ba. Zaɓen Atiku Abubakar ɗan takarar shugaban ƙasa bai shafi kujerar da shugaban jam’iyya ke kai ba. Na ci zaɓe bisa ƙa’idojin da jam’iyya ta shimfiɗa.

“Na maida hankali wajen yin aiki na. Kuma ban damu da masu surutai marasa kan-gado ba.” Cewar Ayu.

Da aka tambaye shi ba ya ganin rikicin da ake yi da ɓangaren Wike zai iya haifar wa PDP rashin nasara a zaɓen 2023, sai Ayu ya ce, “da ni aka kafa PDP, saboda haka wasu tsagerun yara da ba su ma san yadda jam’iyyar ta Keto daji har ta kawo yau, ba su isa su haifar wa jam’iyyar da matsala ba.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin tsauraran sharuɗɗan da Wike ya gindaya idan ana so a shirya.

Bayanan abin da ya faru tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, a taron neman sulhun da su ka yi a Landan, a ranar Alhamis sun fito fili Premium Times ta damƙe.

An taron neman sulhu ɗin ne a otal ɗin Lane Carlton Hotel. Daga cikin zaratan ɓangaren masu goyon bayan Wike, waɗanda suka raka shi zaman sulhun akwai Gwamna Seye Makinde na Jihar Oyo, Samuel Ortom na Jihar Benuwai, Okezie Ikpeazu na Jihar Abiya. Shi kuma Atiku ya na tare da Gwamna Ahmadu Fintiri na Jihar Adamawa.

Taron dai ya zo sa’o’i kaɗan bayan Wike ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da kuma Shugaban Jam’iyyar LP, Peter Obi duk a Landan ɗin. Dama kuma a ranar Litinin ɓangaren Wike ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, wanda shi ma kamar Obi ya ke ƙoƙarin maida Wike ɓangaren sa, domin cin roba daga rigimar cikin gidan PDP, wadda ta rincaɓe tun bayan kammala zaɓen fidda-gwani.

Majiyar PREMIUM TIMES ta ce ɓangaren Wike ya shaida wa Atiku cewa matakin farko kafin a daddale yin sulhu ɗin tukunna, har Wike ya goyi bayan Atiku, sai Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Iyorchia Ayu ya sauka, a gaggauta maye gurbin sa da ɗan kudu.

Sun ce Wike da jama’ar sa ba za su taɓa goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa sannan kuma shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa shi ma daga Arewa.

Ɗaya daga cikin gwamnonin ne ya yi magana a madadin sauran, ya ce wannan sharaɗi na farko su na so a gyara shi ne domin a yi adalci wajen rabon muƙamai. Kuma su na so a gyara da wuri kafin kusantowar zaɓen 2023.

Sannan kuma sun zargi Ayu da rarraba kai ko raba haɗin kan jam’iyya, maimakon kallon da ake yi masa wai wani mai haɗa kan PDP.

Ɓangaren Wike ya ce tun da aka kafa PDP ba a taɓa yin shugaban jam’iyya wanda ya rarraba kawunan ‘yan jam’iyya kamar Ayu ba.

Sun ce maimakon Ayu ya tashi ya nemi haɗin kan kowane ɓangare da sauran hasalallun da ba a yi wa adalci ba, sai ya ƙirƙiri sabon ra’ayin raba kawuna ta hanyar rungumar shugabannin da babu adalci da raba-daidai a cikin sa.

Wike dai ya zargi Ayu da nuna goyon bayan Atiku ƙarara a lokacin zaɓen fidda-gwani.

Ɓangaren Ayu ya ci gaba da cewa tilas Atiku ya tashi ya gyara rashin adalcin da aka yi wajen rabon muƙamai na shugabancin PDP, ta yadda tun a nan idan ya yi haka, to zai nuna da gaske ya ke yi zai iya haɗa kan ‘yan Najeriya kenan idan ya zama shugaban ƙasa.

Majiyar ta ce shi kuma Atiku ya yarda tabbas akwai ɓangarancin miƙa manyan muƙaman PDP a Arewa, to amma ya yi togaciya da cewa dokar PDP ta nuna idan shugaba ya sauka, ba za a iya yin gyaran da su ke so a yi ba, domin idan Ayu ya sauka, wanda zai maye gurbin sa ɗin ma Mataimakin Shugaban Jam’iyya ne na Ƙasa, kuma shi ma ɗan Arewa ɗin ne dai.

Sai dai kuma ɓangaren Wike sun tunatar da Atiku cewa a lokacin da shugaban PDP Okwesilieze Nwodo ya yi murabus cikin 2011 bayan an zaɓi Goodluck Jonathan ya zama shugaban ƙasa, ai ba a ɗauki mataimakin shugaban jam’iyya wanda shi ma a lokacin ɗan kudu ba ne.

Bayan an yamutsa gashin baki sosai a wurin taron, Atiku ya nemi su ɗan ba shi lokaci domin ya tuntuɓi manyan jam’iyya sannan ya waiwaye su.

Majiya ta ce wannan batun ne kaɗai aka tattauna a wurin taron, amma ba a tattauna sauran rashin jituwar da ke tsakanin Wike da Atiku ba.

Tags: AbujaAtikuAtiku AbuabakarDele MomuduHausaMohammed HayatuddeeenNajeriyaNewsPREMIUM TIMESTariela Oliver
Previous Post

GWANJA YA KIRA RUWA: NBC ta haramta wakar ‘Warr’ ta ce wakar bata tarbiyya ce

Next Post

Masu ƙirƙirar ƙarya ne ke cewa akwai saɓani tsakani na da Shugaban APC – Tinubu

Ashafa Murnai

Masu ƙirƙirar ƙarya ne ke cewa akwai saɓani tsakani na da Shugaban APC - Tinubu

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ramalan Yero ya fice daga PDP, ya ce jam’iyyar ta ishe shi haka nan
  • Ba za mu bari a yi mana rinto da rana tsaka ba, mutanen Kaduna mu suka zaɓa – Ashiru
  • TATTALIN ARZIKI: Gwamnatin Tarayya ta tara naira tiriliyan 10.18 a 2022
  • KURUNKUS: Kwamitin Amintattun jam’iyyar NNPP sun kori Kwankwaso daga Jam’iyyar Kwatakwata
  • Kotu ta ci tarar gwamnatin Kano Naira biliyan 30 saboda rusa ginegine ba bisa ka’ida ba

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.