Shugaban Hukumar Kwastan ta Ƙasa Hameed Ali, ya bayyana cewa iƙirarin da NNPCL ya yi cewa a kullum ana shan fetur lita miliyan 60 a Najeriya, ƙarya ce da rufa-rufa kawai.
Ya yi wannan iƙirarin shi ma a ranar Alhamis, lokacin da ya bayyana gaban Kwamitin Majalisar Tarayya Mai Lura da Harkokin Kuɗaɗe.
Ali ya yi wannan kakkausar suka dangane da dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen biyan kuɗaɗen tallafin fetur, kamar yadda NNPCL da Ministar Harkokin Kuɗaɗe su ka bayyana a baya.
Ya ce idan har ana shan fetur lita miliyan 60 a kullum a Najeriya, to me ya sa kuma NNPC ta ce lita miliyan 98 ake fitar wa ‘yan kasuwa a kullum?
Shugaban Kwastan ya ce me ake yi da sauran lita miliyan 38? Ina ake kai su kuma su wa ake bai wa kuɗaɗen tallafin da ake cirewa na lita miliyan 64 da na lita miliyan 38 a kullum?
Ali ya ce bai yiwuwa ma a ce a kullum lita miliyan 60 ɗin ake sha a Najeriya, “domin wanda ya cika tankin sa a yau da yamma, zai yi kwanaki kafin ya sake cika tankin motar ta sa.
“Kuma misali idan aka yi lodin fetur daga Minna zuwa Kaduna, idan aka kai shi gidan mai ai ba a ranar zai ƙare ba.
“Wannan abin takaici ne. Shekarar 2021 mun yi maganar tallafin fetur a wurin nan. Abin haushi kuma ha shi a 2022 mu na sake yin maganar.
Ya ce babban kuskure ne a ce a riƙa ciwo bashi don a biya kuɗin tallafin fetur.
“Ya za a ce za a ciwo bashin sama da naira tiriliyan 11, kuma rabin kuɗin ko ma fiye da rabi su tafi wajen biyan tallafin fetur?
Mataimakin Shugaban Kwamitin Harkokin Kuɗaɗe, Sa’idu Abdullahi ya ce abin damuwa ne ganin yadda biyan maƙudan kuɗaɗe ke kassara tattalin arzikin Najeriya.
Ya ce lallai akwai rinto da gidoga a batun biyan kuɗaɗen tallafin fetur.
Kwanan baya Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed ta ce Gwamnatin Najeriya za ta yi gangamin neman amincewa a cire tallafin fetur.
Ministar Harakokin Kuɗaɗe, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta Ƙasa ta amince a shirya taron gangamin dukkan jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi masu faɗa-a-ji, domin a tattauna yadda za a cimma matsayar yarjejeniyar a cire tallafin fetur.
Zainab ta bayyana haka ranar Alhamis a gaban Kwamitin Majalisar Tarayya mai binciken yadda ake kashe kuɗaɗen tallafin fetur.
Sannan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta yi shirin kashe naira tiriliyan 3.35 wajen biyan tallafin fetur a cikin 2023 daga Janairu zuwa ƙarshen Yuli na shekarar.
Minista Zainab ta ce tunanin a yi gangamin shawara a amincewar ɗaukar matsaya ɗaya kan cire tallafin fetur, batu ne shugabannin majalisar tarayya da ta dattawa su ka bayar shawara.
Daga nan ta ce yanzu haka har an fara tsare-tsaren shirya taron.
Ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya na kashe naira biliyan 18 6 a kullum a ɓangaren fetur, kuma an kashe naira tiriliyan 6.2 wajen biyan tallafin fetur daga 2013 zuwa 201.
Ta ce a cikin watanni shidan ƙarshen wannan gwamnatin za ta kashe naira tiriliyan 3.35 wajen biyan kuɗaɗen tallafin fetur.
Zainab ta ce Gwamantin Tarayya na biyan naira 283.3 a kowace lita ɗaya ta fetur.
“Mun zauna da shugabannin majalisun ƙasa, sun bayar da shawarar me zai hana a yi taron masu ruwa da tsaki da su ka haɗa har da shugabannin jam’iyyun siyasa. Mun gabatar da wannan shawara ga Majalisar Zartaswa, kuma ta amince a fara shirin tsara taron.
“Akwai buƙatar yin wannan taro ya kasance tattaunawa ce ta ƙasa baki ɗaya. Idan ƙasa baki ɗaya ta amince a cire tallafin fetur, to sai a cire ɗin.
“Ba abu da Shugaban Ƙasa zai ce ga yadda za a yi ba. Ba ma’aikatar harkokin kuɗaɗe ce za ta bayar da shawarar yadda za a yi ba.” Inji Zainab.