Saboda jin daɗin yadda Hukumar Hisbah ta Jihar Kebbi ta ”tsaftace jihar daga alkaba’in shaye-shayen giya da karuwanci”, gwamnatin jihar ta maida jami’an Hisbah cikakkun jami’an tsaro a ƙarƙashin hukumar su.
Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Abubakar Bagudu mai suna Yahaya Sarki, ya bayyana cewa Gwamnatin Kebbi da ‘Yan Majalisar Dokokin Jiha da Shugabannin Ƙananan Hukumomi 21 sun bai wa Hisbah gudummawa ta tallafin kuɗaɗen naira miliyan 100, domin su ji daɗin gudanar da aikin su.
Ya ce haƙiƙa Hisbah ta taka muhimmiyar rawar kawar da alfasha a faɗin Jihar Kebbi, musamman a ɓangaren shaye-shayen giya da karuwanci.
Gwamna Bagudu ya ce namijin ƙoƙarin da Hisbah ta yi tsawon shekaru 20 da kafuwar ta a jihar wajen kawar da ayyukan baɗala da sauran manya da ƙananan laifuka ne ya sa gwamnatin Kebbi ta ga ya dace kuma lokaci ya yi da za a maida hukumar Hisbah cikakkun jami’an tsaro.
Ya ce ayyukan Hisbah ba su tsaya ga hana aikata alfasha, shan giya da karuwanci kaɗai ba. Ya ce Hisbah ta yi nasarar cusa wa matasa ɗa’a da ɗora al’umma bisa hanya madaidaiciya.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kebbi, Babale Yauri ya ce ya gamsu da gagarimar nasarar da Hisbah ta cimma a tsawon shekaru 20 da kafa ta a Jihar Kebbi.
Yauri ya lissafa kaɗan daga cikin nasarorin da Hisbah ta samar a jihar, waɗanda a ce sun haɗa da rufe gidajen sayar da harasa, rufe gidajen karuwai, ceton jariran da aka tsallake aka bari da daƙile sauran ayyukan masha’a.
Discussion about this post