Jam’iyyar PDP ta naɗa Gwamna Aminu Tambuwal Babban Daraktan Kamfen ɗin Atiku Abubakar na yaƙin neman zaɓen 2023.
Tambuwal zai jagoranci mutum 326 da ke cikin rundunar kamfen ɗin, wadda aka kafa makonni biyu kafin a fara yaƙin neman zaɓen ‘yan takarar shugaban ƙasa.
An kuma naɗa Gwamna Udom Emmanuel na Jihar Akwa Ibom matsayin Shugaban Majalisar Kamfen ɗin Atiku Abubakar.
Sanarwar da Umar Bature ya fitar a ranar Alhamis, ta ce Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Kamfen (na Arewa), sai Gwamna Seyi Makinde na Oyo Mataimakin Shugaban Majalisar Kamfen na Kudu.
Gwamna Nyesom Wike da sauran gwamnonin PDP duk Mambobi ne a cikin majalisar.
An dai naɗa wannan kwamitocin biyu ne tun ba a kai ga sasanta rikicin da ke faruwa tsakanin Gwamna Wike da Atiku Abubakar, inda ya ke yaƙin cewa tilas sai dai a cire Shugaban PDP, Iyorchia Ayu a naɗa ɗan Kudu.
A wata sabuwa kuma, ‘yan Najeriya sun ce shirin Atiku na danƙara naira tiriliyan 7 ga tattalin arziki, ƙarambosuwa ce kawai da shafa-labari-shuni.
A ranar Talata ce ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar ya ƙaddamar da Daftarin Ceto Tattalin Arziki Ƙasa (ESF), wanda ya ce zai yi amfani da shi idan ya zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Atiku ya ƙaddamar da daftarin a Cibiyar Hada-hadar Cinikayya da Masana’antu ta Legas (LCCI).
A cikin daftarin akwai alƙawurran danƙam wanda Atiku ya yi wa ‘yan Najeriya, masu ƙunshe da yadda zai ceto ƙasar daga matsalolin da su ka dabaibaye ta.
Sai dai kuma wanda ya fi jan hankalin ‘yan Najeriya shi ne Daftarin Ceto Tattalin Arzikin Najeriya (Economic Stimulus Fund).
A ƙarƙashin wannan daftari dai Atiku ya yi alƙawarin danƙara naira tiriliyan 7, wato dala biliyan 10 a cikin harkokin tattalin arziki a kwanakin sa 100 na farkon kama mulki, idan har aka zaɓe shi.
Da ya ke Atiku ya watsa daftarin a cikin shafin sa na Tiwita, cikin kwana ɗaya an samu fiye da mutum 4,500 waɗanda su ka shiga su ka bayyana ra’ayin su.
Akasarin waɗanda su ka yi magana duk caccakar Atiku su ka yi.
Kusan ra’ayin sauran ya yi daidai da ra’ayin wani mai suna Faisal Kaita, wanda ya fara da cewa, “Shin a ina kuɗin su ke waɗanda Atiku zai zuba a cikin kwanaki 100 na farkon mulkin sa idan ya ci zaɓe?
“Ko kuwa ya na nufin sake nitso za mu yi ciki neman bashi, kamar yadda mu ke fama a wannan gwamnati ta yanzu?”
Faisal Kaita ya yi wannan tsokaci ne saboda ganin cewa a yanzu haka Najeriya na fama da rashin kuɗi, rashin Isasshen kuɗaɗen shiga da kuma ɗimbin biyan bashin da ta ke yi duk wata, wanda a can mafi yawan kuɗaɗen haraji da na fetur ɗin ta ke tafiya.
Shi kuma wani mai suna Mark Logam, tambayar Atiku ya yi ya ce a ina zai samo kuɗin? “Ko a cinikin ɗanyen mai za ta ɗebi kuɗaɗen ne?”
Wasu kuma cewa su ka riƙa yi wannan duk tatsuniya ce da shafa-labari-shuni da kuma ƙarambosuwa ta Atiku kawai.
“Yaushe ƙasar da ke fama da rashin tsaro za ta danƙara mata naira tiriliyan cikin kwanaki 100 na farkon mulkin ka, idan ka ci? Ya ƙasa za ta inganta idan babu tsaro? Shi kuma tsaron sai bayan shekara nawa da hawan ka sannan za ta samar da shi?”
Discussion about this post