• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    Ƴan ta’adda sun gamu da fushin sojojin Najeriya, sojoji sun kashe 50 sun kama 60

    GRAINS MARKET AT KAFIN MADAKI DISTRICT IN GANJUWA

    Yari ya raba tallafin tirela 145 cike maƙil da buhunan masara 145 ga mabuƙata a Zamfara

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

GUMURZUN 2023: Atiku ya maida wa Bataliyar Wike raddi bayan sun janye daga Rundunar Mayaƙan PDP 2023

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
September 21, 2022
in Rahotanni
0
ƘURUNƘUS: Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP

Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya yi mamaki sosai, jin cewa Gwamna Nyesom Wike na Ribas da tawagar sa sun janye daga kwamitin yaƙin neman zaɓen ATIKU 2023.

Cikin wata sanarwa daga Atiku, ya ce yayin da abin da Wike da tawagar sa su ka yi ya ba shi mamaki sosai, a gefe ɗaya kuma ya ce shi a kankin kan sa ba zai iya tilasta wa Shugaban PDP Iyorchia Ayu ya sauka ba, har sai idan shi Ayu ɗin ne da kan sa ya saura don ra’ayin kan sa.

Atiku ya ce bai yiwuwa a tilasta wa Ayu sauka, kamar yadda ɓangaren Wike ya jajirce sai an yi, sai fa ta hanyar da dokar ƙasa da dokar jam’iyyyar PDP ta tanadar.

Dangane da janyewar su kuwa, Atiku ya ce ya yi mamaki, domin in banda ‘yan kwamitin da aka zaɓa daga Jihar Ribas, na sauran jihohin da su ka goyi bayan Wike, duk uwar jam’iyya ta jihohin su ce ta gabatar da sunayen su.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Bataliyar Wike ta janye daga Rundunar Yaƙin Atiku 2023.

Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Atiku Abubakar 2023 ta afka cikin ruɗani, yayin da bataliyar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas ke jagoranta ta janye jiki daga shiga yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar ɗin.

Wannan janyewar da su ka yi ta zo ne daidai saura mako ɗaya a fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, wanda INEC ta bayar da iznin fara fafatawa daga ranar 28 ga Satumba.

Sanarwar ta fito ne daga bakin ɗaya daga cikin zaratan Wike, kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Olabode George.

Bode George ya yi sanarwar bayan sun kwashe tsawon ranar Talata zuwa washegarin Laraba su na ganawar sirri a gidan Gwamna Wike da Fatakwal.

Daga cikin mayaƙan da su ka halarci taron janyewa daga rundunar Atiku 2023, akwai Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, Olabode George, tsoffin gwamnoni irin su Segun Mimiko, Ayo Fayose, Donald Duke, Ibrahim Ɗanƙwambo, Jonah Jang da tsohon Ministan Shari’a, Mohammed Adoke.

Akwai kuma tsohon Minista Jerry Gana da Shugaban PDP na yankin Kudu maso Kudu, Dan Orbih, sai tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, Chibudom Nwuche da wasu hamshaƙan PDP da dama.

Ɓangaren Wike ya ce ba zai shiga kamfen ɗin Atiku ha har sai Shugaban Jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu ya sauka daga muƙamin sa, an naɗa ɗan Kudu, domin a yi adalcin raba-daidai.

Wani jigon PDP dai ya ce tun farko Ayu ne janyo saɓani da Wike, domin bai kamata ya gidan gidan Tambuwal yin godiyar haɗa-bakin yin nasarar Atiku a zaɓen-fidda-gwani ba.

Wani jigon PDP kuma fitaccen lauya, Obunike Ohaegbu, ya bayyana cewa a gaskiya tun farko dai Shugaban PDP Iyorchia Ayu, ya tafka kuskure da ya je har gida ya yi wa Gwamna Aminu Tambuwal godiyar haɗa kai da ya yi da Atiku Abubakar aka kayar da Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas a zaɓen fidda gwani.

Ohaegbu ya bayyana wannan ra’ayi na sa a cikin wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talabijin na AIT, a ranar Alhamis.

Idan ba a manta ba, bayan Atiku ya yi nasarar kayar da sauran ‘yan takara, Shugaban PDP Ayu ya samu Tambuwal har Gidan Gwamnatin Jihar Sokoto washegari, inda ya yi masa godiya, saboda ya ce dukkan magoya bayan sa su zaɓi Atiku.

An yi ittifaƙin cewa janyewar da Tambuwal ya yi ce ta sa Atiku ya samu yawan ƙuri’un da ya kayar da Wike.

Tun daga nan kuma Wike ya riƙa kiran su Tambuwal da Ayu maciya amana.

Sannan kuma kwana biyu bayan zaɓen fidda gwani, Wike ya ce janyewar da Tambuwal ya yi ba bisa ƙa’ida ya yi ta ba, ta zo a makare. Har ya ce “da na dama da na hargitsa taron zaɓen fidda gwanin PDP.” Inji Wike.

Tun daga ranar da Ayu ya kai wa Tambuwal ziyara, har yau jam’iyyar ba ta zauna lafiya ba.

Wike ya koma gefe tare da goyon bayan wasu gwamnonin PDP na kudu, su na neman a tsige Ayu domin a cewar da ya fito daga Arewa, yanki ɗaya da Atiku Abubakar.

Sai dai kuma yayin da ake ƙoƙarin sasantawa, yanzu kuma PDP ta naɗa Tambuwal Babban Daraktan Kamfen na yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar. Wannan lamari ko kaɗan ba zai yi wa Wike daɗi ba.

“Babban kuskure ne a nuno Ayu ya je godiya gidan Tambuwal, har ana watsawa a gidan talabijin da sauran kafafen soshiyal midiya.” Inji Ohaegbu.

Tags: AbujaHausajihar OyoLabaraiNewsOlabode GeorgePDPPREMIUM TIMESSeyi MakindeTambuwalWike
Previous Post

SAI GANI SAI HANGE: Ƙabilar Igbo ba su da wata damar yin shugaban ƙasa a zaɓen 2023 -Orji Kalu

Next Post

Muna yi wa kiristocin yankin Arewa kaf hudubar kada su zaɓi Tinubu da Shettima saboda musulmai ne – Babachir

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Tir da zaɓen musulmi mataimaki da Tinubu yayi, tun yanzu ya san APC ta sha ƙasa a zaɓe – Babachir

Muna yi wa kiristocin yankin Arewa kaf hudubar kada su zaɓi Tinubu da Shettima saboda musulmai ne - Babachir

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru
  • TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa
  • FCT ABUJA: Wike ya kori shugabanni da daraktocin hukumomi 21
  • Kotu ta yi watsi da ƙarar PDP a Shari’ar gwamnan Kaduna, dalili kuwa shine wai ba ta shigar da ƙara da wuri ba
  • MASHAHURAN JAMI’O’IN DUNIYA: Jami’ar Bayero ta fita kunya, Covenant da UI ne kawai ke gaba da ita a Najeriya

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.