Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa Sanata Uba Sani ya bayyana yadda ya tallafa wa ƙananan ƴan kasuwa da zunzurutun kuɗi har naira miliyan 20 domin su iya siyan shaguna a kasuwannin da gwamnatin jihar Kaduna ta sabonta a faɗin jihar.
Sanata Uba wanda shine ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar APC ya bayyana haka ne a jawabin da yayi wa kungiyoyin ƴan kasuwan Kaduna da suka kawo masa ziyara a jihar.
” Mun baiwa kananan ƴan kasuwa waɗannan kuɗaɗe ne domin su iya biyan kashi 10% na mallakar shago a sabbin kasuwannin. Kuma in Allah ya yarda zan ci gaba da taimakawa ƙananan ƴan kasuwa da jari domin su bunƙasa kasuwanci da sana’o’in su.
Ƙungiyoyin Ƴan kasuwa daga kananan hukumomi 23 ne suka yi gangamin kaf ɗin su domin yi wa takarar Uba Sani mubaya’a da nuna goyon baya ga takararsa na neman zama gwamnan jihar Kaduna a 2023.
Bayan haka sanata Uba ya bayyana wa dandazon mutane a wurin taron cewa a matsayin sa shugaban kwamitin Harkokin Kudi ya samar wa mutum akalla 12,000 kanana da matsaikaitan basussuka daga babban bankin Najeriya a matsayin tallafi a gare su.
Ya ce ” Wannnan abu da nayi somin ta ɓi ne, zan fadada shi fiye da yadda muka somo a baya. Sannan ina muku godiya bisa wannan karamci da kuk nuna min.
Discussion about this post