Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa duk da ƙalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta da kuma rigingimun cikin ƙasa, hakan bai hana tattalin Nijeriya bunƙasa da ci gaba ba.
Buhari ya ce tattalin arzikin ƙasa gaba ya ya ke yi ba baya ba, yayin da ya ke jawabi wurin ƙaddamar da Kwamitin Shugaban Ƙasa Mai Bada Shawara kan Tattalin Arziki.
Ya ƙaddamar da kwamitin na PCNE ranar Juma’a, a Abuja.
Buhari ya ce annobar korona da yaƙin Ukraniya da Rasha da asarar ɗimbin ɗanyen man fetur, sun haifar wa tattalin arzikin Najeriya naƙasu sosai.
“Duniya ta yi fama da manyan ƙalubale a cikin shekaru ukun nan, tun daga kullen korona, wanda ya tsaida komai, kuma ya haifar da tashin gwauron zabin farashin kayan abinci da kayan masarufi a duniya.
“Sai kuma daidai lokacin da ake ƙoƙarin fita daga ƙuncin korona, yaƙi ya ɓarke tsakanin Rasha da Ukraniya, wadda ya haifar wa duniya wata babbar matsalar da har yau ake ƙoƙarin ganin an warware ta.
“Amma kuma duk da ƙalubalen da ake fuskanta, tattalin arzikin mu gaba ya ke ci ba baya ba.”
Buhari ya magana a kan matsalar taguwar ɗnayen man da Najeriya ke haƙora da ya ce a Agusta 2022 an riƙa haƙo ƙasa da ganga miliyan ɗaya.
Ire-iren waɗannan matsaloli inji Buhari ke haddasa tilas ake fita ramto kuɗaɗe domin aikata ayyukan inganta rayuwar al’umma.
Ya ce Gwamnatin sa a ta ci gaba da inganta rayuwar al’umma musamman ta ƙarƙashin Shirin Inganta Rayuwar Marasa Galihu (SIP).
Dangane da yawan ciwo bashin da gwamnatin sa ke yi, ya ce wannan ba abin damuwa ba ne, domin kuɗaɗen da ake ramtowa ana yin ayyukan raya ƙasa da raya al’umma ne da su, musamman ayyukan more rayuwa, inganta lafiya da sauran ayyukan inganta rayuwar masara galihu.
“Yayin da ‘yan Najeriya ke nuna damuwa dangane da yawan ciwo basussuka, to kuma kamata ya yi a gode mana saboda ai basussukan da mu ke ciwowa, mu na yin ayyukan inganta rayuwar al’ummar ƙasar nan da su, musamman inganta lafiya, inganta ƙasa da sauran ayyukan inganta rayuwar al’umma.
Discussion about this post