Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta cafke wata mata mai mukamin ‘Reverend Sister’ a Coci mai suna Maureen Wechinwu dake harkallar cinikayyar yara kanana.
Vanguard ta wacce ta buga labarin ta ce Maureen kan siya wadannan yara ta siyar da su ga wanda yake bukata a fadin kasar nan.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Friday Eboka ya ce rundunar ta kama Maureen a gidanta dake kauyen Aluu a karamar hukumar Ikwerre da yara 15 a gidan.
Rundunar ta samu wannan nasara ne bayan samun bayanan sirri kan aiyukkan da matar ke yi a kauyen.
Ya ce yaran da rundunar ta ceto na da shekara 7 zuwa 9 sannan ya ce da zaran sun kammala gudanar da bincike za a kai ta kotu domin yanke mata hukunci.
Eboka ya ce yaran sun dauki tsawon awa 24 kafin suka iya yin magana da ‘yan sanda saboda a tsorace suke ganin yadda Maureen take gallaza musu a zaba.
Yaran da aka yi garkuwa da su
Sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa an yi garkuwa da wadannan yara a bangarori dabandaban na jihohin dake Kudu maso kudancin kasar nan.
Daga cikin yara 15 din da aka ceto iyaye biyar sun zo sun karbi ‘ya’yan su.
1. An yi garkuwa da Prosper Godwin ranar 31 ga Oktoba 2020 a kasuwar Ikpazasia dake jihar Bayelsa tare da wasu yara biyu da bai san inda aka dauko su ba.
An siyar da Prosper wa wata mata a jihar Legas amma daga baya aka dawo da shi hannun Maureen.
2. An yi garkuwa da Queen Harry a Ojukwu filed Mile 1, Diobu dake Fatakwal da misalin karfe 7 na dare.
3.An yi garkuwa da Miracle John Ohiri ranar 19 ga Nuwambar 2021 a hanyar Ada-George dake Fatakwal tare da mahaifiyarta da kannanta biyu.
Zuwa yanzu babu wanda ke da masaniyar inda mahaifiya da kanan Miracle suke.
Mahaifin Miracle John Ohiri ya tabbatar da haka bayan rundunar ta kira shi, ya tabbatar cewa a lokacin da iyalansa suka bace ya Kai kara a ofishin ‘yan sandan dake Rumuokpakani.
4. An sace Favour Edeze a hanyar zuwa kasuwan Creek dake Fatakwal ranar 29 ga watan Afrilu 2022 da misalin karfe 10 na safe.
Mahaifin yarinyar Emeka Edeze ya tabbatar wa rundunar yadda aka sace ‘yarsa Favour.
5. An yi garkuwa da Chimele Obinna ranar 24 ga Afrilu 2022 yayin da take wasa da kanwarta a kofar gidan su dake Rumuodara/Culvet Oroigwe a Fatakwal.
Mahaifiyar yarinyar Glory Obinna ta ce ta kai karar sace ‘yarta ofishin ‘yan sandan dake Okporo.
Rundunar ta yi kira ga mutane musamman wadanda ‘ya’yan su suka bace da su hanzarta zuwa ofishin ‘yan sanda domin duba ‘ya’yan su.
Discussion about this post