Dubban magoya baya da masoyan ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP ne suka yi tattaki a manyan titunan babban birnin tarayyar Najeriya fomin nuna goyon bayan su ga dan takarar.
Pete Obi na daga ciki gaggan ƴan takara da ke neman ɗarewa kujerar shugabancin Najeriya bayan wa’adin shugaba Buhari ya cika a 2023.
Sai dai kuma matasa da musamman mutanen yankin kudancin Najeriya, Kudu Maso Gasa, sun lashi takobin ganin Obi ya lashi zaɓen.
A garin Abuja ranar Asabar dubban magoya bayan Obi sun yi dandazo a manyan tituna domin nuna goyon bayan su ga ɗan takarar.
A wani zaɓen sanin ra’ayoyin mutane da aka gudanar a shafilan sada zumunta a yanar gizo, Peter Obi ne ya nuna ƴan Najeriya za du zaɓa a zabe mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar LP Julius Abure ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa dubban mutanen da ya gani a wannan tattaki bai zo masa da mamaki ba saboda ya san cewa ƴan Najeriya na neman canji kuma sun ganta a jam’iyyar LP a wurin Peter Obi.
” Mutane na tara kuɗin daga aljifansu daga naira 1000 zuwa 10,000, wasu na bada motocin su kyauta wasu kuma gidajen su don tafiyar Peter Obi. Wannan tafi akwai nasara kuma za ku ce na faɗi muku.
Duk da cewa Obi da Mataimakin sa Baba-Ahmed ba su halarci taron nuna goyon bayan ba, sun aika wa masoyan su sakon godiya.
” Muna Kano domin cigaba da ganawa da mutane, amma ina mika godiyar mu ga dukka masoyan mu. Dafatan burin mu zai cika.
Discussion about this post