Daga ranar Juma’a ce 2 ga Satumba dokar haramta haya da baburan Okada za ta fara aiki gadan-gadan a Legas.
Dokar dai ta tanaji ɗaurin shekaru uku ga ɗan Okada, shi ma fasinjan da aka ɗauka za a ɗaure shi shekaru uku.
Haka kuma dokar ta bada ikon a ƙwace babur ɗin ɗan Okada a mitsitstsike shi a gaban jama’a.
Kwamishinan Harkokin Sufuri na Jihar Legas Frederick Oladeinde ne ya bayyana haka lokacin da ya gana da manema labarai a ranar Laraba, a Ikeja.
Ya ce daga ranar Juma’a za a fara kama duk wani wanda ya karya dokar ana ɗaurewa.
A ta bakin sa, ƙananan hukumomi da yankunan da aka haramta haya da baburan su haɗa da Kosofe (Ikosi-Isherin da Agboyi-Ketu).
Akwai kuma Ƙaramar Hukumar Mushin, inda aka haramta haya a Odi-Olowo. Sai Oshodi a yankin Oshodi Isolo da Ajigbo.
A Shomolu an hana a Bariga. Duk wanda aka kama ya ce babu rangwame, sai ya yi zaman kurkuku.
Oladeinde ya yi kira ga jama’a su bayar da halin kai domin a samu nasarar bin dokar.
Ya ce an tanaji jami’an LASTMA 200 domin su riƙa yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran jama’an tsaro domin tilasta bin dokar da kuma damƙe kangararru.
Discussion about this post