Hukumar NDLEA ta yi kamun da bata taɓa yin irin sa ba a Najeriya inda ta kama wani gida sukutum da ake harkallar hodar Ibikis a jihar Legas.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi ya ce an kama katan-katan din hodar iblis da aka naɗe su a baƙaƙen kwaleya domin safara su ziwa kasashen waje.
Gidan na rukunin gidajen attajirai dake Ikorodu, jigar Legas.
An kama tan 1.8tons (1,855 kilograms) na hodar iblis da aka yi wa kuɗi naira N194,775,000,000.
Gagariman ƴan harkallar kwayoyin da aka kama sun haɗa da Soji Jibril, 69, ɗan asalin garin Ibadan, Jihar Oyo, Emmanuel Chukwu, 65, daga Ekwulobia, jihar Anambra, Wasiu Akinade, 53, daga Ibadan, jihar Oyo, Sunday Oguntelure, 53, daga Okitipupa, jihar Ondo da Kelvin Smith, 42, dan kasar, Jamaica.
Kuma dukkan su ƴan kungiyar gaggan masu safarar muggan kwayoyi ne na duniya da ake ta bibiya ana neman a kama tun daga 2018.
Idan ba a manta rundunar ta kama wani ƙasurgumin mai safarar kwayoyi wanda ya saka hodar iblis cikin kwalaben turare.