PREMIUM TIMES ta tattauna da wanin tsohon faston cocin Angilika kan dalilin da ya sa ya daina aikin fasto ya koma yin wa’azi kan karin aure a addinin Kirista.
Faston mai suna Lotanna Ogbuchukwu ya yi karin haske kan dalilin da yasa ya kafa kungiyar da mahimmancin da kara aure ke da shi a rayuwar mutum bisa sharuɗɗan addinin kiristan ci.
PT: Baya ga ra’ayin ka na kara aure akwai wani dalilin da ya sa ka fice daga aikin fasto daga cocin Angilika?
Ogbuchukwu: A’a dalilin kenan da ya sa na fice daga coci saboda bana so na ci gaba da zama a wurin da akidar su bai zo dai-dai da nawa ba.
PT: Ka ce an yi maka wahayi kan karin aure a addinin kirista, ko za ka iya bayyana lokacin da aka yi maka wannan wahayin da yadda wahayin ya zo?
Ogbuchukwu: Na fara samun wahayi kan tabbaci da ingancin yin mace fiye da ɗaya a addinin kirista shekaru 20 da suka gabata a lokacin ina kungiyar masu yada bushara na yara kanana a cocin Angilika sai dai a lokacin ban fahimci wahayin da aka yi mini ba sosai, sai bayan shekaru 3 zuwa 4 ne na fahimci wahayin sannan ko a lokacin babban abin da na fi fargaba da shine shin haka din gaskiya ce sannan menene mutane za su ce akai idan na daɗi.
Amma hakan bai hana ni cigaba da kokarin ganin na wayar wa mutane kai bisa ga karantarwar addinin kiristanci na halasta airen fiye da mace ɗaya.
PT: Amma akidar ka na yin auren mace fiye da daya a addinin kirista ya saba wa abin da Littafi Mai Tsarki ya fada na auren mace daya?
Ogbuchukwu: Ki jira zuwa lokacin da zan fara karantarwa kan karin aure a addinin kirista. Da yaddan Ubangiji zan fara karantar da mutane ranar Lahadi a YouTube a yanar gizo sannan na ci gaba kowani Lahadi.
PT: Shin ko akwai fastocin da suka mara maka baya a lokacin da ka fice daga coci ko Akwai wadanda za su mara maka baya yanzu?
Ogbuchukwu: A’a ban sanar da kowa ba a lokacin da zan fice daga coci sannan ko lokacin da na Saka bidiyon a YouTube kan sanarwar barin aiki a coci, cocin bata san haka ba.
Buri na shine na samar wa kiristocin da suka tabbatar sun aikata zunubi ta hanyar fasikanci ko zina mafita. Saboda coci bata iya samar wa mutane irin haka, kuma mafita shine su iya kara aure.
PT: Menene fastoci irin ka suka yi bayan da suka samu labarin sabuwar fatawar ka?
Ogbuchukwu: Kamar yadda na ce ban tattauna da kowa ba.
PT: Menene ra’ayin matar ka game da akidar ka?
Ogbuchukwu: Kamar yadda na fada a baya ban tattauna da kowa ba kafin na kafa wannan kungiya.
PT: Akwai adadin yawan matan da ya kamata namiji za iya aura?
Ogbuchukwu: Duk za ki iya samun wannan bayanai a karantarwar da zan fara a shafin YouTube.
PT: Lokacin da ka bar aiki yaya mambobin ka suka yi?
Ogbuchukwu: Da dama daga cikinsu sun kira sun tambaye ni abin da ya faru.
Kafin na bar aiki gaba daya na fara hutun shekara daya domin na fahimci abin da wahayin da aka yi min ya ke nuna fi.
Bayan na kammala ne na gabatar da wasikar barin aiki.
Mutane da dama sun ce Allah zai dawo da ni kan hanya madaidaiciya wasu kuwa sun ce babu wanda ke bukatar ya saurari karatu na. Kowa dai da ra’ayinsa amma komai zai bayyana bayan na fara karantarwa.
PT: Mahaifin ka ya auri mata da yawa ne?
Ogbuchukwu: A’a.
PT: Idan wani yazo neman auren Ƴarka a matsayi mata ta biyu ko ta uku za ka amince?
Ogbuchukwu: Kwarai kuwa domin abin da nake koyar wa mutane ke nan.
Abin da nake kara jadaddawa mutane shine kada su zam fasikai, su rika yin zina kafin su yi aure.
Discussion about this post