Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Ƙasa ta ‘Sibil Defens’, Ahmed Audi, ya bayyana dalilan da su ka sa ba za a kafa dokar bai wa ‘yan Najeriya damar riƙe bindiga ba.
Audi ya bayyana cewa a yanzu ma da ba bayar da damar ba, kuma ba a kafa dokar iznin ba, bindigogi sun yawaita ga hannun jama’a, har sun zama alaƙaƙai, to ina ga idan an ba kowa iznin mallaka.
Audi ya yi wannan bayanin a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).
Ya ce kafin a kai lokacin da za a bai wa jama’a damar mallakar bindiga a ƙasar nan, sai ilmi ya ƙara ratsa jama’a da kuma wayar da kai sosai tukunna.
“Ko a Amurka da Turai inda ake bada damar da mutum ya kai munzilin damar fara tuƙa mota, zai iya mallakar lasisin bindiga, yanzu ana taka-tsantsan, saboda yadda ake amfani da bindigogi a ƙasashen ana yin aika-aika.
“Musamman a Amurka, haka kawai mutum zai ɗauki bindiga ya shiga makaranta ya buɗe wa ɗalibai ƙananan yara wuta, ya yi ta kashe su.” Inji Audi.
Haka nan kuma ya yi bayani dalla-dalla kan yadda Hukumar ‘Sibil Difens’ ta kafa rundunar mata domin tsaron makarantu 81,000 masu fuskantar barazanar tsaro a faɗin ƙasar nan.
Kwamanda-Janar na Hukumar Tsaro ta NSCDC (Sibil Difens’) Ahmed Audi, ya bayyana cewa an kafa Rundunar Mata ta jami’an tsaron ne domin tura su wasu daga cikin makarantun ƙasar nan 81,000 da ke kan siraɗin barazanar tsaro.
Audi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya yi da shi a Abuja.
Ya ce an kafa Rundunar Mata ce bayan an yi wani ƙwaƙƙwaran nazarin ɗaukacin makarantun ƙasar nan baki ɗaya.
“Mun yi binciken ne domin gano adadin yawan makarantun da mu ke da su a faɗin ƙasar nan, kuma domin sanin adadin guda nawa mu ke da su waɗanda za a iya cewa ba su fuskantar barazanar tsaro.
“Idan na ce waɗanda ba su da matsalar tsaro, to ina nufin waɗanda ke da jami’an tsaro ko dai daga cikin ɓangarorin tsaro na gwamnati ko kuma jami’an tsaro masu zaman kan su? Kuma shin an kewaye makarantun da katanga ko shingen waya, ko kuwa?
“Bayan mun yi wannan gagarimin bincike, sai mu ka fahimci gaskiya akwai matsala a ƙasar nan ta rashin tsaro a makarantu. Saboda adadin yawan makarantun da mu ka gano ba su da tsaro su na da yawan da lamarin ya tayar mana da hankali sosai.
“A ce dai ga mu da makarantu sama da 81,000 waɗanda ko shingen waya ko katangar da ta kewaye makarantun babu. Sannan kuma babu jami’an tsaro, wannan lamari babba ne sosai,” inji shi.
Audi ya ci gaba da cewa wannan bincike da su ka yi ya bai wa Hukumar NSCDC ƙarin hasken yadda za su bijiro da ƙwaƙƙwaran shirin samar da tsaro a makarantun.
Sai ya ce saboda haka kafa rundunar mata na ɗaya daga cikin matakan samar tsaron, kasancewa kuma an gano yadda ake yawan yi wa mata fyaɗe, da kuma yawaitar garkuwa da ɗalibai da kuma malamai ana karɓar kuɗaɗen fansa.
“Ka san mugayen da ke aikata wannan aiki na amfani da fyaɗe su na razana mutane.
“Da zarar mata sun ji an ambaci fyaɗe, to za su ɗauki batun da muhimmanci da muka damuwa sosai.
“Saboda haka sai mu ka ce za mu kafa rundunar mata su yi yaƙi da wannan gagarimar matsalar sosai da sosai. Kuma mu ka gane cewa mata ne za su fi yin wannan jajirtaccen aiki da gaske.
“Don haka ne mu ka kafa ƙasaitacciyar rundunar mata ta NSCDC, waɗanda sojoji ne su ka ba su horo da atisaye, kuma aka ƙara masu ƙaimi da azamar kare ɗalibai a makarantu da su kan su makarantun.
“Saboda haka mu na da wannan rundunar a faɗin ƙasar nan, jihohi daban-daban.” Inji Audi.
Audi ya ce zaratan NSCDC na da horo sosai na daƙile duk wata matsalar tsaro. Sannan kuma ya ce tasirin su shi ne kowace ƙaramar hukuma a faɗin ƙasar nan akwai su a dukkan ƙananan hukumomi 774 na Najeriya da kuma cikin yankunan karkara.
“Tasirin NSCDC na biyu kuma shi ne, jami’ai ne da su ka samu hoto daga ɓangaren hukumomin sojoji daban-daban.
“Domin ko lokacin Yaƙin Basasa daga 1967 zuwa 1970 lokacin da aka fara aiki da jami’an mu, mun riƙa kasancewa a bayan sojoji, mu na taimaka masu ta hanyar kula da waɗanda su ka samu raunuka, kuma mu na ba su duk taimako da kulawar agajin da ya kamata a bai wa dakaru a fagen yaƙi.”
Ya ce saboda haka tura dakaru mata a makarantun ƙasar nan ya rage garkuwa da ɗalibai da malaman su.
Discussion about this post