Hukumar Hisba ta Kano ta bayyana cewa ta maida mabarata akalla 805 garuruwansu a kananan hukumomi 44 na jihar.
Kwamandan hukumar Hisbah na jihar Haruna Ibn-Sina ya sanar da haka wa manema labarai ranar Juma’a a hedikwatar hukumar dake Sharada.
Haruna ya ce daga cikin mutum 805 din da aka maida garuruwansu akwai mata 536 da maza 279 kuma duk ‘yan asalin jihar Kano ne.
Haruna ya ce an maida mabarata da yawa da suka zo jihar Kano daga wasu jihohin kuma tuni an hada su da yan uwan su.
Haruna ya ce mutum uku daga cikin mabaratan da suka maida jihohin su uku sun kamu da cutar kanjamau ‘yan mata da dama daga cikin su duk an dirka musu ciki sannan kuma wasu da kullin damin kudi masu yawan gaske a cikin takacen su.
” Mafi yawan mabaratan da muka kama mun kama su a kan titunan jihar, wasu a karkashin gada a kasuwa, wasu a tashar jirgin ƙasa da dai sauran wurare.
” Bayan haka muna ciyar da wadanda muka killace abinci sau uku a rana tun da muka kam su.
Sannan kuma hukumar ta gargadi duk wani mabaraci da ya koma kan titunan jihar har aka kama shi to lallai za a maka shi a kotu domin ya karya dokar jihar ce.
” Mun gano akwai masu yin sane da sace sacen wayoyin mutane da sunan wai su mabarata ne. Saboda haka ba za mu lamunta wa wanda duk muka kama.
Discussion about this post