Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya naɗa Abdulhamid Dembos, shugaban gidan talabijin na kasa NTA.
Sanarwar hakan na kunshe ne a wata sanarwa wanda ministan yaɗa labarai Lai Mohammed ya saka wa hannu ranar Laraba a garin Abuja.
Kafin nadin Dembos shugaban NTA, shi ne babban darektan fannin kasuwanci na gidan talabijin ɗin.
Wannan naɗi na tsawon shekaru uku ne a zangon farko.
Dembos ya taba rike shugaban NTA na Lokoja da Kano, kafin ya rike shugaban NTA na shiyyar Arewa a Kaduna.
Bayan haka ya taɓa rike kujerar shugaban kungiyar RATTAWU na kasa.
Discussion about this post