Shugaba Muhammadu Buhari ba ɗora laifin rashin ci gaban Najeriya da matsalar tsaro a kan manyan ‘yan bokon ƙasar nan.
A ranar Talata ya bayyana haka, lokacin da ya ke buɗe wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnatin jihar Imo ta gina a Owerri.
Buhari ya buɗe tituna da ginin Majalisar Dokokin Jihar Imo, wanda aka sake ginawa.
Buhari ya ce Najeriya ba ta cimma ci gaban da ta yi ƙoƙarin cimmawa ba, saboda manyan ‘yan bokon ƙasar ba su taimake ta ba.
“Gaskiya zan faɗa maku ni ‘yan boko na ke ɗora wa laifin kasa zama su yi zurfin tunani da nazarin yadda za su bunƙasa ƙasar mu.
“Tsakanin 1999 da 2015, lokacin da mu ka hau gwamnati, idan mutum ya je ya bincika zai ga a kullum ana haƙo gangar mai miliyan 2.1 kuma ana sayar da kowace ganga dala 100 a lokacin.
“A lokacin da ake samun waɗannan kuɗaɗen masu yawa, an yi watsi da komai. Ku dubi ayyukan raya ƙasa, dubi titin jirgin ƙasa, duk sun lalace a lokacin. Har yanzu ku dubi yadda mu ke ta gaganiya da fannin wutar lantarki, har yanzu ana ta laluben yadda za a magance matsalar.” Inji
Ya ce a lokacin da ya ke ta ƙoƙarin bunƙasa ci gaban ƙasa a gwamnatin sa, ya samu cikas daga matsalar tsaro wadda ta hana gwamnatin sa saket, kuma ta hana haƙo ɗanyen mai.
Ya ce lokacin da ya hau mulki Boko Haram na riƙe da wasu yankuna. Amma kawowa yanzu babu sauran wani yanki a hannun su.
Buhari ya gode wa Gwamnan Uzodinma saboda namijin ƙoƙarin da ya yi wajen raya jihar Imo.
Shi ma Gwamna Uzodinma ya jinjina wa Buhari, inda ya ce “ba don ‘karamar Buhari’ ba da yanzu ‘yan bindiga da ‘yan iskan gari sun mamaye Jihar Imo
Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodinma ya bayyana cewa ba don Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gaggawar kai ɗaukin tsaro a jihar ba, da tuni ‘yan bindiga da waɗanda ya kira ‘yan iskan gari sun mamaye Jihar sa.
Uzodinma ya yi wannan bayani a lokacin da Buhari ke buɗe titi falan-biyu wanda ya tashi daga Owerri zuwa Orlu a ranar Laraba.
Gwamnan ya gode wa Buhari wanda ya ce shugaba ne mai ƙaunar al’ummar Igbo, musamman jihar Benuwai.
Ya ce babu abin da zai ce wa Buhari sai godiya, domin a cikin shekarar ban ya kai ziyara jihar sau biyu.
“Tun bayan yaƙin Basasa ba a yi shugaba guda ɗaya wanda ya yi aiki ɗaya na kwatankwacin maƙudan kuɗi har naira biliyan 360 ba, sai Buhari.”
Uzodinma na magana ne kan aikin Gadar Kogin Neja wadda Gwamnantin Buhari ke aikin ginawa, gadar da ta haɗa Arewacin Najeriya da Kudu maso Gabas.
Ya ce, “Buhari ya yi aikin ƙwarai da nuna kishi. Ba don ya yi gaggawar kai ɗaukin tsaro a Imo ba, da yanzu ‘yan bindiga da ‘yan iska sun mamaye jihar.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Dattawan ƙabilar Igbo za su sake bijiro da neman a saki Nnamdi Kanu don a zauna lafiya a yankin, yayin zaman su da Buhari a Imo.
A ranar Talace Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka Owerri, domin ziyarar buɗe wasu ayyukan raya jiha da Gwamna Hope Uzodinma ya aiwatar.
Buhari ya isa Jihar Imo wajen 11:30 na safe, inda Gwamna da wasu manyan jihar su ka tare shi a filin jirgi.
Cikin ayyukan da ya ƙaddamar har da titi mai hannu biyu, mai tsawon kilomita 36, wanda ya tashi da Owerri zuwa Orlu da kuma wani irin sa mai tsawon kilomita 50 da ya tashi daga Owerri zuwa Okigwe.
Daidai rubuta wannan labari Shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da manyan dattawan ƙabilar Igbo a Owerri, inda ake sa ran za su tattauna batutuwa da dama waɗanda su ka shafi yankin Kudu maso Gabas.
Daga cikin abin da za su tattauna, ana sa ran akwai matsalar tsaron da ta addabi yankin, ciki har da jihar Imo, inda fanɗararrun IPOB ke kai wa jami’an tsaro hare-hare.
Sannan kuma ba za a rasa sake tattauna batun neman da za su sake ba, na a saki Nnamdi Kanu, wanda tsare shi da aka yi ne musabbabin tashe-tashen hankula a yankin.
A cikin watan Nuwamba 2021, Dattawan Ƙabilar Igbo sun tura wakilai wurin Buhari, domin neman a saki Kanu.
Da farko Buhari a ce zai yi tunani kuma ya duba ya gani. Amma kuma daga baya sai ya ce ba zai tsoma baki a lamarin da ke gaban kotu ba.
Discussion about this post