Kassaaɓar da Gwamna Nyesom Wike ya yi a ƙarshen makon nan inda ya yi iƙirarin cewa akwai wani a Fadar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari mai ɗaure wa Shugaban PDP Iyorchia Ayu da Atiku Abubakar gindi su na yin abin da su ka ga dama a cikin PDP, ta taso da wasu batutuwan da su ka faru watannin baya zuwa yanzu.
Yin duba a dajin da APC ta keto kafin ta kai ga yin zaɓen fidda gwanin ‘yan takarar shugaban ƙasa a ranar 9 Ga Yuni, zai iya sa duk mai hangen nesa kuma mai waiwayen baya yin tunanin cewa kalaman da Wike ya yi sun yi kama da karin maganar Hausawa da su ke cewa, “biri ya yi kama da mutum.”
Wike ya ce, duk wani bobbotai da Ayu ke yi, ya na taƙama ne da wani a Fadar Shugaban Ƙasa mai ɗaure masa gindi shi da Atiku.
“Ba zan faɗi sunan sa a yanzu ba, amma akwai lokacin da zan bayyana sunan sa kuma a lokacin da ya dace.” Cewar Wike.
Idan haka ne kuwa, to kenan ba a rasa masu don yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu maƙarƙashiya.
Ya kamata mai karatu ya yi duba kan abin da ya faru daga watanni takwas zuwa yau aka APC da kuma halin da ta shiga har ranar da jam’iyyar ta yi zaɓen fidda gwani.
A lura cewa Wike wanda babban burin sa shi ne ya ga cewa mulki ya koma kudu, kuma dalili kenan shi ma ya shiga takara, bai ji daɗin kayar da shi da Atiku ya yi ba, alhali shi a ganin sa da ba a shirya masa tuggu ba, shi zai kayar da Atiku a zaɓen fidda gwani.
Ya na cikin rikici da Ayu da Atiku sai aka ji ya dira Landan ya gana da Bola Tinubu, wanda shi ma gogarma ne sukutum na neman mulki ya koma hannun kudi, kuma a hannun sa.
Babu wanda ya san abin da su ka tattauna tsakanin su a Landan. Wasu na ganin kasancewa su biyu duk su na son mulki ya koma Kudu, don haka mai yiwuwa sun bayyana wasu sirrukan ɓoye waɗandaba kowa ya sani ba, ciki za ta iya kasancewa har da zargin makusantan Buhari na ɗaure wa Atiku gindi shi da Ayu Shugaban PDP.
Idan an tuna, farkon bayyanar ‘yan takarar APC, an riƙa yin raɗe-raɗin cewa wasu ‘yan takara da su ka haɗa Godwin Emefiele na CBN, Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan da Sanata Ahmad Lawan, cewa Majalisar Dattawa.
Yayin da Emefiele domin su ka har kotu ya garzaya cewa ya na da ‘yancin tsayawa takara, a gefe guda kuma Buhari bai ja masa kunne ba, domin a lokacin bai sauka daga muƙamin sa ba kamar yadda doka ta tanadar, sai kuma labari ya bazu cewa wasu gaggan APC sun goyi bayan a tsayar da ɗan Arewa takara a APC, domin ɗan kudu ba zai iya kayar da Atiku Abubakar na PDP ba.
Ana cikin wannan kuma sai aka riƙa cewa Buhari ya na goyon bayan Ahmad Lawan, inda an sai da ta kai Shugaban APC Abdullahi Adamu ya iƙirarin cewa Lawan ne ɗan takarar APC, kuma shi Buhari ke goyon baya.
An sacce iskar takarar Lawan ne yayin da Gwamnonin APC su ka tsaya kai da fata cewa sai dai a bai wa ɗan kudu takarar shugaban ƙasa a APC.
Katoɓara Da Bobbotan Tinubu A Abeokuta:
Masu lura da siyasar Najeriya da dama na ganin cewa Tinubu ya yi hargagin da ya yi a Abeokuta ne kafin zaɓen fidda gwani, saboda wataƙila ya gano maƙarƙashiyar neman hana shi takara.
To sai dai kuma duk da a bisa dukkan alamu Shugaba Buhari bai riƙe shi a zuciya ba, bayan gorin da shi Tinubu ɗin ya yi masa a Abeokuta, akwai makusantan Buhari da har yau su na jin haushin Tinubu, kamar yadda wasu da dama ke hasashe. Zai iya yiwuwa su ne ke ƙoƙarin yi wa takarar Tinubu maƙarƙashiya, ba tare ma da sanin Buhari ba.
Yadda Tinubu ya fara yunƙurowa ya na nesanta kan sa daga zargin mallakar wasu kantama-kantaman kadarori da kamfanoni a ƙasar nan, shi ma alama ce mai nuna cewa ya fara rama duka ne ko kuma ya fara kare kan sa daga masu yi masa yarfen siyasa da zargin mallakar kadarorin da ba su cikin adadin da ya yi rantsuwar ya mallaka.
Ko ma dai me kenan, a bisa dukkan alamu kokawar da Wike ke yi shi da Ayu da Atiku, akwai alamun tirje-tirje na iya kai su ga bangazar APC, wacce garin kallon ruwa, ta saki baki har kwaɗo ya yi mata ƙafa.
Discussion about this post