Rayuwar DPO na ‘Yan Sandan Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ta iyalan sa na cikin hatsari, yayin da ‘yan bindigar da su ka yi garkuwa da shi su ka yi barazanar kashe shi idan ba a biya su naira miliyan 20 fansar da su ka nema ba.
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da DOP Sani Mohammed, bayan sun tare shi kan babban titin Birnin Gwari a Jihar Kaduna, lokacin da ya ke kan aikin sa.
Ƙanin sa mai suna Adamu Abdullahi ya shaida wa wakilin PREMIUM TIMES a yau Lahadi cewa ‘yan bindiga sun ce idan ba a cika masu nairs miliyan 13 ba, to za su kashe shi a ranar Laraba mai zuwa.
Abdullahi ya ce tun da farko sun nemi a biya su naira miliyan 20, “amma mun saida duk wani abu da ya mallaka, mun kai naira miliyan 7 da kyar. Kuma sun ƙi sakin sa.
“A yau kwanakin sa 69 a hannun su. Mun je Hedikwatar ‘Yan Sandan Kaduna har sau uku, amma har yanzu babu wani ƙwarin guiwa daga gare su. Kuma har yau rundunar ‘yan sanda ba ta tura tawaga ta je wa iyalan sa jaje ba.
“Sai da ta kai mun ƙwace wayoyin matar sa da na ‘ya’yan sa, saboda a duk lokacin da ‘yan bindiga su ka kira su, su na yi masu barazanar cewa za su kashe DPO ɗin. Nan take matar sa ke suma da ta ji sun faɗi haka.
“Yanzu haka shi ma mahaifin sa, wanda dattijo ne mai shekaru 90, ya na cikin matsanancin halin jimamin abin da ɗan sa ke ciki.
Abdullahi ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari, Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya da Kwamishinan ‘Yan Sandan Kaduna su yi azamar kuɓutar da DOP Sani Mohammed daga hannun ‘yan bindiga.
Kakakin ‘Yan Sandan Kaduna Mohammed Jalige ya ce su na bakin ƙoƙarin su, kuma ba za su shaida wa jama’a irin ƙoƙarin da su ke kan yi ba.
Discussion about this post